| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Mali ta ɗaure jami'in diflomasiyyar Faransa shekara 20 a gidan yari kan zargin neman haddasa rikici
Mali na zargin jami'in na ƙasar Faransa da aiki tare da Hukumar Leƙen Asiri ta Faransa domin neman hargitsa ƙasar.
Mali ta ɗaure jami'in diflomasiyyar Faransa shekara 20 a gidan yari kan zargin neman haddasa rikici
Hoton birnin Bamako na kasar Mali da aka dauka daga sama. / Reuters

Wata kotu a Mali ta yanke wa wani jami'i a ofishin jakadancin Faransa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 20 kan zargin yin leƙen asiri da “zagon ƙasa ga tsaron ƙasa”.

An tsare shi tun lokacin da aka kama shi a watan Agustan 2025, kuma a ranar Alhamis an ci tarar sa da dalar Amurka 6,225 tare da hana shi shigowa Mali na tsawon shekaru 20.

A lokacin da aka kama shi, hukumomin Mali sun zargi jami'in, wanda aka bayyana da sunan shi da Yann V., da aiki ga hukumomin leƙen asirin Faransa, sannan hukumomin na Mali sun soki “ƙasashen waje” da ke ƙoƙarin kawo rashin kwanciyar hankali a ƙasar.

An tsare shi a ranar 13 ga Agusta tare da wasu jami'an Mali da ake zargin suna shirya juyin mulki a ƙasar.

Faransa ta sake jaddada cewa tuhumar da ake yi wa jami'in, wanda yake aiki a ofishin jakadancin Faransa a babban birnin Bamako, ba ta da tushe.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Faransa a ranar Jumma’a ta ce: “Ma’aikacinmu na fuskantar shari'a kan tuhume-tuhume marasa tushe.”

“Jami'inmu yana aiwatar da aikin haɗin gwiwar tsaro kuma a kowane hali Faransa ba ta taka rawa ba — kai tsaye ko a kaikaice — wajen lalata zaman lafiyar Mali,' in ji ma'aikatar.

Rumbun Labarai
Guinea ta nemi Faransa ta mayar da ƙoƙon kawunan 'yan ƙasarta masu fafutuka
Ƙoƙarin kawar da sankarau: Manufar Afirka ta kawar da cutar baki ɗaya nan da 2030
Mutane fiye da 4,000 ne suka kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo - Gwamnati
Kwamitin tattaunawa na Libiya ya cim ma matsaya kan tsarin ɗaukar shugaban hukumar zaɓe
Gargadin shugabannin Afirka kan cin abinci a makare da illolin shan siga da giya
Shugaba Biya na Kamaru ya yi sauye-sauye a shugabancin sojin ƙasar
Ghana ta amince da ɗaurin shekara 20 ga duk wanda ya mayar da gonar koko zuwa wani abu daban
Ɗaruruwan mutane sun yi hijira daga kudu maso yammacin Nijar saboda hare-haren 'yanta'adda
‘Yan Boko Haram sun kashe sojojin Nijar, in ji kafar watsa labaran gwamnati
Fitacciyar mawaƙiyar Afirka Ta Kudu ta soke kalankuwarta a Legas bayan an kori baƙi daga ƙasarta
Gwamnatin Ghana ta amince da shawara ƙara wa'adin mulkin shugaban ƙasa
Adadin 'yan ci-ranin da suka rasu ya kai 19 bayan dubbai sun tsallaka zuwa yankin Ceuta na Sifaniya
Biranen Afirka 25 da Amurka za ta rufe ayyukan bayar da biza daga ranar 1 ga Agustan 2026
Siyasar Kamaru: Ina Shugaba Paul Biya ya shiga?
Nijar ta dakatar da kamfanonin dillancin siminti 36 kan zargin ɓoye shi don haddasa ƙarancinsa
Hukumomin Libya a Benghazi sun kori baƙin-haure fiye da 117,000 daga ƙasar
Mutumin da ya fi kowa tsawo a Ghana Awuche ya rasu
Chadi ta sanar da shirin fita daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC)
An gudanar da zanga-zanga a Tripoli saboda tsadar rayuwa da tabarbarewar ayyukan gwamnati
Ƙarin ma'aikatan jinya sun shiga yajin aiki yayin da cutar Ebola ta kama kusan mutum 3,000