| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
Ɗanwasan film ɗin Breaking Bad Giancarlo Esposito ya karɓi Musulunci a Saudiyya: rahoto
A cewar Al-Sheikh, shawarar da ɗan wasan ya yanke ta biyo bayan kyawawan abubuwan da ya fuskanta yayin zamansa a Saudiyya da mu'amalarsa da Musulmai yayin aiki a wani aikin samar da shiri a ƙasar.
Ɗanwasan film ɗin Breaking Bad Giancarlo Esposito ya karɓi Musulunci a Saudiyya: rahoto
Wani bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta ya nuna ɗanwasan yana yin sallah tare da 'yan tawagar ɗaukar shiri a cikin masallaci, in ji rahoton. / AFP

Ɗanwasan kwaikwayon Amurka Giancarlo Esposito, wanda aka fi saninsa da rawar da ya taka a matsayin Gus Fring a shirin fim ɗin nan mai dogon zango na Breaking Bad, ya karɓi Addinin Musulunci yayin zamansa a Saudiyya , in ji rahotannin kafafen watsa labarai.

Saudi Gazette a ranar Lahadi ta ruwaito cewa Shugaban Hukumar Nishaɗi, Turki Al-Sheikh, ya ce Esposito ya furta Shahada, kalmar shaidar imani ta Musulunci, kuma ya shiga sallah tare da 'yan tawagar ɗaukar shirin fim a wani masallaci yayin da suke ɗaukar fim a masarautar.

A cewar Al-Sheikh, shawarar da ɗan wasan ya yanke ta biyo bayan kyawawan abubuwan da ya fuskanta yayin zamansa a Saudiyya da mu'amalarsa da Musulmai yayin wani aikin ɗaukar fim a ƙasar.

Ya kuma ce Esposito ya nuna godiya ga al'ummar da karimcin bakuncin da ya tarar da su yayin ɗaukar fim ɗin.

Wani bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta ya nuna ɗanwasan yana yin sallah tare da 'yan tawagar ɗaukar shiri a cikin masallaci, in ji rahoton.

Esposito ya yi nisa sosai a harkar fina-finai da talabijin kuma ya yi fice saboda rawar da ya taka a Better Call Saul, The Mandalorian, da sauran ayyuka.

Rahoton ya ce ya samu shahara a duniya tare da samun ɗumbin zaɓaɓɓun lambobin yabo saboda yadda ya taka rawa a matsayin Gus Fring.

A cewar Saudi Gazette, Esposito a halin yanzu yana cikin aikin ɗaukar fim na Seven Dogs, ɗaya daga cikin manyan ayyukan da ake haɓakawa yayin da Saudiyya ke faɗaɗa ɓangarorin nishaɗi da fina-finai da kuma ƙoƙarin jawo hankalin manyan ayyukan ƙasashen waje da ƙwararru.