Ci gaban Afirka ya dogara ne kan al’ummarta mazauna ƙasashen waje ba wai a tallafi ba

Fiye da mutane miliyan 170 'yan asalin Afirka sun kafa wata al’umma mai girma da albarkatu a ƙasashen waje, sai dai ba a amfana sosai daga tasirinsu.

By
'yan Afirka mazauna ƙasashen waje sune mabuɗin ci gaban da zai iya sauya nahiyar ta fuskar tattalin arziki, ilimi, da al'adu. / Others

A mafi yawan lokuta akan ba da labarin ci gaban Afirka ta fuskoki ban-daban: ta hanyar samun taimakon ƙasashen waje, lamuni, da sauye-sauyen gwamnati. Sai dai ba a cika tuna da ɗaya daga cikin manyan hanyoyin ci gaban nahiyar da ke bayan iyakokinta ba: wato ‘yan nahiyar da ke zaune a ƙasashen waje.

A yanzu haka, fiye da mutane miliyan 170 'yan asalin Afirka sun kafa wata al’umma mai girma da albarka a ƙasashen waje, sai dai ba a amfana sosai daga tasirinsu. An takaita gudunmawar da suke bayarwa ga iya kuɗaɗen da suke aikowa gida.

Sai dai a yanzu, labarin ya wuce nan: a fannin tattalin arziki, da ilimi, da al'adu, 'yan Afirka mazauna ƙasashen waje sun zama tamkar injin ɗin ci gaba da zai iya canza nahiyar.

Idan aka yi la'akari da yawan kuɗaɗen da ake turo wa daga ƙasashen waje, Bankin Duniya ya ce, a shekarar 2021 an tura dala biliyan 49 zuwa nahiyar Afrika.

Zuwa shekarar 2024, an kiyasta cewa ƙuɗaɗen sun kusan ninka zuwa dala biliyan 95 adadin da ya zarce tallafin ƙasashen waje da dama. ƙasar Masar ($22.7 biliyan) da Nijeriya ($19.8 biliyan) suna cikin manyan ƙasashe da ke karɓar kuɗaɗen waje.

Iyalai da dama suna dogara ne kan waɗannan kuɗaɗe don sayen abinci, da kuɗin makaranta, da kula da lafiya, da biyan sauran buƙatu na gida. Sai dai duk wannan kaɗi kaɗai ba zai iya gina tattalin arziki ba.

Idan aka ƙarkatar da wani ɓangare zuwa ga saka jari mai amfani zai iya sake fasalin hanyar ci gaban Afirka.

Bankin Raya Afirka (AFD) ya nuna buƙatar samar da tsare-tsare masu kyau na saka hannun jari, tare da rage shingayen dokoki, da hanyoyin hada-hadar kuɗaɗe da za su iya mayar da hanu baka- hanun ƙarba zuwa ayyukan haɓaka tattalin arziki, matsalar ba wai son yin bane amma samar abubuwan da hanyin yinsu.

Jarin ilimi wani muhimmin bangare ne

An daɗe ana kwatance kan abin da ake kira "ficewar kwararru" daga Afirka zuwa ƙasashen waje a matsayin wata asara ga nahiyar. Amma binciken da aka yi kwanan nan ya nuna akasin haka.

Wani bincike da aka gudanar a shekarar 2023 kan nazarin ci gaban duniya ya nuna ‘‘brain circulation,’’ wato yadda kwararru a ƙasashen da ba na su ba suke ba da gudummawa ta hanyar ba da shawarwari na ɗan wani lokaci da jagoranci ta hanyar intanet da koyarwa ta haɗin gwiwa da kuma yin ayyuka na musamman a wani fanni ba tare da sun koma kasar gabaƙi ɗaya ba.

Waɗanda suka dawo ƙasarsu ta asali sun kan tawo da ilimi da fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire da za su ƙarfafa wa harkokin shugabancin gida, cibiyoyi da kuma koƙarin ci gaban zamani. Gwamnatocin Afrika za su iya cin moriyar wannan damar ta hanyar sauƙaƙe amincewa, da karɓar ilimi ko karatu daga ƙasashen waje, da kuma kafa Ƙungiyar kara ilimi ta waɗanda ke ƙasashen waje don tura ƙwararru zuwa wasu fannoni masu muhimmanci.

Bangaren kasuwanci yana da matuƙar ɗaukar hankali.

'Yan Afirka da ke kasuwanci a ƙasashen waje suna da fahimtar kasuwannin cikin gida yayin da suke ƙara sanin yanda kasuwannin yankunan Yamma, da Asiya, da kuma Gabas ta Tsakiya suke.

Su ne gadar da ke haɗa kamfanonin Afirka da na ƙasashen duniya, da kasuwancin fitar da kayayyaki da kuma hanyoyin saka jari. Amma duk da haka ƙasashe da dama ba sa samar da yanayi mai sauƙi da zai bai wa ‘yan ƙasarsu damar saka jari ko gina kasuwancinsu.

 Jinkiri wajen tsare-tsare samun takardar shaida zama ɗan ƙasashe biyu da kuma wahalar rejistar kamfanoni da tsoffin dokokin saka jari duk suna daga cikin ƙalubalen da ake fuskanta. Samar da wani sashen kasuwanci a Ofisoshin jakanci da ake da su a ƙasashen waje da kuma sauƙaƙa hanyoyin samun shaida zama ɗan ƙasa da kuma ƙarfafa saka hannun jari za su iya taimaka wa wajen bunƙasa kasuwanci a faɗin nahiyar.

Tasirin al’adu wani ɓangare da tuni mazauna ƙasashen da ba na su ba suke taka rawa

Salon Afrobeat ta mamaye jadawalin waƙokin duniya. Nollywood, masana'antar fina-finai ta Nijeriya, yanzu haka ita ce ta biyu mafi girma a duniya a fannin shirye-shiryen da ake yaɗawa. Kazalika masu zane-zanen kayan kwalliya na Afirka suna jagorantar manyan taron ƙawa na Paris, da Milan, da New York.

Al'ummomin Afirka a ƙasashen waje suna haɓaka waɗannan masana'antu, suna faɗaɗa kasuwannin duniya yayin da a ɓangare guda suke ɗaɗa bunƙasa tattalin arzikin Afrika.

A cewar binciken da Friedrich-Ebert-Stiftung ya yi, gudummawar da ‘yan Afrika mazauna ƙasashen waje ke bayar wa yana da matukar tasiri ga cinikayyar kayayyakin al’adu na gida da kuma yadda ake kallon Afrika a ƙasashen duniya.

Bai kamata a yi watsi da tasirin siyasa ba

Al'ummomin Afirka a ƙasashen waje suna tsara manufofi kan ƙaura, da adalci a yanayi, da kasuwanci da kuma ci gaba. Idan aka haɗa su ciki dabara, za su iya zama muryar Afirka a manyan tarukan duniya - ko da kuwa babu shugabannin Afirka a wuraren.

Matsalar ba wai ta rashin iyawa ba ce, sai dai rashin nahiyar ta janyo mutanenta a jiki. Tallafi kaɗai ba zai ƙarfafa hanyoyin farfaɗowar Afirka ba. Makomarta tana kan haɗa kan ‘yan Afirka a gida da kuma waje, don a iya amfana da jarinsu da ƙwarewarsu da kuma tasirin al’adunsu.

Afirka ba ta buƙatar ta sake fasalinta. Tana buƙatar ta ɗauki 'yan nahiyar mazauna ƙasashen waje a matsayin abokan hulɗa ba wai bare ba: a mastayin masu zuba jari, da masu ƙirƙire-ƙirƙire, da jakadu na al'adu, kana masu fafutuka.

Alamomi sun yi nuni da cewa a shirye al’ummomin Afirka a duniya suke, sai dai tambayar ita ce ko a shirye nahiyar take, don su hadu a tsakiya.

Lokaci ya yi da za a ɗauki mataki, da tsare-tsaren manufofi masu ƙyau da hannayen jari da hanyoyin ƙarin ilimi, ‘yan Afirka mazauna ƙasashen waje za su iya zama injin ɗin haɓaka sauye0sauyen tattalin arziki da al’adun Afirka.

Ci gaban Afirka ya dogara ne kan al’ummominta mazauna ƙasashen waje ba wai a tallafi ba.

 Marubucin, Dr. Sunny Ofehe, shi ne babban Mataimakin Gwamnan Jihar Delta kan Hulɗa da kuma Harkokin 'Yan Kasashen Waje.