Shugaban Hukumar Kare Haƙƙin Bil'adama ta MDD ya yi gargaɗi kan jerin sabbin laifuka a Kordofan

Tun daga 25 ga Oktoba, lokacin da RSF ta ƙwace garin Bara a Kordofan ta Arewa, ofishin kare haƙƙin ɗan’adam na MDD ya rubuta aƙalla mutuwar farar-hula 269 sakamakon harbin sama, harbin artilleriya da kisan gaggawa.

By
An ci gaba da kai mumnanan hare-hare a cikin jihohin Kordofan uku a cikin 'yan makonnin da suka gabata / Reuters

Shugaban Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan’adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi gargaɗi a ranar Alhamis cewa yana fargabar "aikata jerin sabbin laifuka" a Sudan a yayin da rikice-rikice masu tsanani ke ƙaruwa a fadin yankin Kordofan, inda Sojojin Ƙasar Sudan da dakarun rundunar RSF da na SPLM-N ke fafatawa.

Tun daga 25 ga Oktoba, lokacin da RSF ta ƙwace garin Bara a Kordofan ta Arewa, ofishin kare haƙƙin ɗan’adam na MDD ya rubuta aƙalla mutuwar farar-hula 269 sakamakon harbin sama, harbin artilleriya da kisan gaggawa.

Sakamakon katsewar sadarwa da intanet da ke hana isar da rahotanni, akwai yiwuwar ainahin adadin ma ya wuce yadda ake faɗa, kamar yadda Volker Turk ya bayyana a cikin wata sanarwa.

A cewar sanarwar, ofishin ya samu rahotannin kisan ramuwar gayya, tun daga kan tsare jama’a ba bisa ka'ida ba da garkuwa da mutane da cin zarafi ta hanyar lalata da tilasta shiga aikin soja — ciki har da yara.

Turk ya ce an kama mutane da yawa bisa zargin "haɗa kai" da ƙungiyoyin adawa, yayin da maganganu na ƙiyayya ke ƙara saka fargabar ƙarin tashin hankali.

"Da gaske abin firgita ne ganin tarihi na sake maimaituwa a Kordofan ba da jimawa ba bayan mummunan abin da ya faru a Al Fasher," in ji shi. "A lokacin, al'ummar duniya sun tsaya tare, sun yi tir da waɗannan barnace-ɓarnace da zalunci. Dole ne mu hana Kordofan zama wani sabon Al Fasher."

An ci gaba da kai mumnanan hare-hare a cikin jihohin Kordofan uku a cikin 'yan makonnin da suka gabata. A ranar 3 ga Nuwamba, rahotanni sun ce jirgin sama mara matuki na RSF ya kai wani hari a wasu tantuna na masu zaman makoki a El Obeid ya inda ya kashe mutane 45, mafi yawansu mata. A ranar 29 ga Nuwamba, an ce harin sama da SAF ta kai a Kauda, Kordofan ta Kudu, ya kashe akalla mutane 48, mafi yawan su farar hula, in ji sanarwar.

Kadugli da Dilling a Kordofan ta Kudu suna ci gaba da kasancewa cikin ƙunci sakamakon rundunonin RSF da SPLM-N, an tabbatar da yunwa a Kadugli yayin da ake ganin yiwuwar yunwa a Dilling. Birnin El Obeid yana kewaye a ta ɓangare da RSF, kuma "duka bangarorin sun toshe hanyoyin shiga na agajin jin kai."

Fiye da mutane 45,000 sun gudu daga gidajensu cikin watan da ya gabata, in ji Turk, yana neman a ba da hanyoyin aminci, a kare ma'aikatan jinƙai da kuma gyara hanyoyin sadarwa.

Ya yi kira ga ƙasashen da ke da tasiri su dakatar da shigowar makamai da ke ƙara hura wutar rikicin.