Netanyahu ya bayar da umarnin ƙara zafafa hari kan Iran saboda tsoron Trump na iya dakatar da yaƙin
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya umarci sojojin ƙasar su hanzarta kai hare-hare ta sama a Iran tsawon awanni 48 domin lalata masana'antar makaman ƙasar gwargwadon iyakar abin da za su iya kafin Trump ya dakatar da yaƙin.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya umarci sojojin ƙasar su hanzarta kai hare-hare ta sama a Iran tsawon awanni 48 domin lalata masana'antar makaman ƙasar gwargwadon iyakar abin da za su iya kafin Washington ta fara shirin tsagaita wuta, in ji New York Times.
Wannan umarni ya biyo bayan yadda gwamnatinsa ta samu kwafin wani daftari mai ɗauke da buƙatu 15 da Amurka ta tsara don kawo ƙarshen yaƙin, inda aka ga cewa a cikin buƙatun babu wani cikakken shiri na magance shirin nukiliyar Iran ko kuma makamanta masu linzami.
Jami'an Isra'ila na tsoron Shugaban Amurka Donald Trump zai iya bayyana fara tattaunawar zaman lafiya a kowane lokaci, in ji rahoton.
Game da shirin da aka ruwaito, mai magana da yawun Fadar White House, Karoline Leavitt, ta yi kira a yi taka-tsantsan, tana mai cewa ta ga wani shiri "da aka yada a kafafen watsa labarai" amma Fadar ba ta taba tabbatar da shi ba.
"Akwai wasu abubuwa na gaskiya a ciki, amma wasu daga cikin labaran da na karanta ba su cika zama na gaskiya ba," kamar yadda ta ƙara da cewa.
Netanyahu ya bayar da wannan umarnin yayin wani taro a hedkwatar soja ranar Talata, bayan manyan kwamandoji sun gabatar da taƙaitaccen bayani kan wuraren da har yanzu za a iya kai hari.
Ƙarancin tasiri
Gaggawar ta nuna wani matsi da Isra'ila ke fuskanta a cikin wannan yaki, a cewar jami'an tsaron ƙasa na Isra'ila da aka ambata a rahoton.
Shawarar kawo ƙarshen yakin a hannun Trump take, wanda ya bar Netanyahu da ƙarancin tasiri wajen yadda za a kawo ƙarshen sa.
Kawunan jami'an Isra'ila sun rabu; wasu na neman a ƙara aƙalla wani mako ana kai ƙarin hare-hare, yayin da wasu ke so a kawo ƙarshensa cikin gaggawa.
Jami'an da aka ambata sun ce manyan nasarorin soja sun fi yawa ne a makon farko, yayin da damuwa ke ƙaruwa game da ra'ayin duniya, kuɗin da yaƙin ke lashewa da nauyin da ke kan 'yan Isra'ila.
Muhawarar tayar da zaune-tsaye
Trump ya yi watsi da ra'ayin da Firaminista Netanyahu ya gabatar na ƙarfafa wa jama’ar Iran gwiwa a fili su tayar da zaune tsaye a Iran, in ji Axios.
Netanyahu ya ba da shawarar a ƙarfafa 'yan Iran su fito kan tituna a wani kiran da ya yi na kwanan nan, amma Trump ya yi adawa da ra'ayin, yana gargaɗin cewa za a iya daƙile masu zanga-zangar," in ji rahoton, kamar yadda masu ruwa da tsaki daga Amurka da Isra'ila waɗanda ke da masaniya a kan lamarin suka bayyana.
Rahoton ya ƙara da cewa jami'an Isra'ila sun yi imanin cewa hare-haren kwanan nan da aka kai kan manyan jami'an Iran na iya raunana gwamnati, kuma su haifar da yanayi na tashin hankali.
Amurka da Isra'ila sun kaddamar da yaƙinsu na haɗin gwiwa kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, inda aka kashe fiye da mutane 1,340.
Iran ta mayar da martani da hare-hare a fadin yankin, wanda ya kawo cikas ga jigilar mai da zirga-zirgar jiragen sama.