An kashe sojoji 15 a harin 'yanta'adda a Jamhuriyar Benin

Ƙungiyar ‘yanta’addan mai alaƙa da Al Qaeda ta ɗauki alhaƙin kai harin da aka kai ranar Laraba a wani sansani kusa da Kofouno, da ke iyakar ƙasar da Jamhuriyar Nijar.

By
Aƙalla sojoji 15 aka kashe a wani harin 'yan ta'adda a Benin, in ji soji ranar 5 ga watan Maris, 2026 / Reuters

'Yanta'adda masu alaƙa da ƙungiyar Al Qaeda sun kashe sojoji 15 a wani hari da suka kai a wani sansanin soji a arewacin Jamhuriyar Benin, kamar yadda rundunar sojin ƙasar ta bayyana ranar Alhamis.

Ƙungiyar ‘yanta’addan mai alaƙa da Al Qaeda ta ɗauki alhaƙin kai harin da aka kai ranar Laraba a wani sansani kusa da Kofouno, da ke iyakar ƙasar da Jamhuriyar Nijar.

Mai magana da yawun soji, Kanal James Johnson ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP ranar Laraba cewa harin ya jikkata sojoji biyar, “amma ba sa fuskantar barazanar mutuwa."

Wata majiyar soji wadda aka tura yankin ta shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa harin ya laƙume rayuka da yawa, inda take magana bisa sharaɗin sakaye sunanta.

"A halin yanzu muna kan share yankin," in ji majiyar.