Hukumar Kula da Sadarwa ta Nijeriya (NCC) da Hukumar Kare Farar-Hula ta Nijeriya (NSCDC) sun gargadi kamfanonin gine-gine da sauran masu ayyukan injiniya da su guji lalata layukan sadarwa na ƙarƙashin ƙasa na fibre-optic yayin aikin gyaran hanyoyi da sauran ayyukan gine-gine, inda suka ce masu aikata hakan na iya fuskantar hukunci a kotu.
Hukumomin sun bayyana cewa ba za a lamunci ci gaba da lalata layukan sadarwan ba, wanda galibi ana yi ne saboda da sakaci inda suka jaddada cewa lalata layukan laifi ne.
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa, NCC da NSCDC sun bayyana layukan sadarwan na ƙarƙashin ƙasa a matsayin muhimman kadarorin ƙasa, waɗanda ke tallafa wa tattalin arzikin fasahar zamani na Nijeriya da harkokin kasuwanci da kuma kuma taimaka wa sadarwar gwamnati.
Sun yi gargaɗin cewa lalata waɗannan kayayyakin more rayuwar na iya jefa tsaron ƙasa zaman da tattalin arziki da lafiyar jama’a cikin hadari.
Hukumomin sun ƙara da cewa, karkashin dokar kare kayayyakin sadarwa masu muhimmanci na ƙasa ta (CNII) Order 2024, an ayyana layukan sadarwar na fibre-optic a matsayin muhimman kayayyakin sadarwa na ƙasar.
Saboda haka, idan an lalata su sakamakon haƙar ƙasa ko ayyukan gini ko kuma rashin tutuɓar hukumomin da abin ya shafa, hakan zai iya zama aikata laifi.
Sun ƙara da cewa duk wanda aka samu da laifi — ko mutum ɗaya, kamfanin gine-gine ko dan kwangilar gwamnati — zai fuskanci hukunci da sauran matakan doka kamar yadda dokoki suka tanada..
















