Filin jirgin saman Sabiha Gokcen na Istanbul ya karɓi fasinja fiye da miliyan 44 a cikin wata 11

A shekarar 2023, filin jirgin saman ya karɓi fasinja miliyan 33.7 tsakanin watannin Janairu zuwa Nuwamba.

By
“A watanni 11 kawai, mun wuce adadin fasinjoji miliyan 41.4 da aka samu a gaba daya shekarar 2024,” in ji wani jami'i / AP

Filin jirgin saman Sabiha Gokcen na birnin Istanbul ya karɓi fasinja miliyan 44.2 tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamban bana, adadin da ya ɗara na bara inda ya karɓi fasinja miliyan 41.4.

Ministan Sufuri da Harkokin More Rayuwa Abdulkadir Uraloglu ya ce an samu wannan nasara ce saboda wani sabon titin jirgin sama da aka ƙaddamar a watan Disamban shekarar 2023, wanda hakan ya sa manyan jirage suna iya sauka a filin jirgin saman.

Kuma sakamakon hakan ya sa aka samu ƙaruwa wajen yawan fasinjojin da ke amfani da filin jirgin saman.

Ministan ya bayyana hakan ne lokacin bikin cika shekaru biyu da ƙaddamar da sabon titin jirgin saman.

A shekarar 2023, filin jirgin saman ya karɓi fasinjoji miliyan 33.7 tsakanin watannin Janairu zuwa Nuwamba.

“An samu ƙaruwar fasinja da kaso 31 cikin 100 waɗanda suka yi amfani da filin jirgin saman a watanni 11 na shekarar 2025, idan aka kwatanta da kafin samar da sabon titin jirgin saman a shekarar 2023,” in ji ministan.

“A watanni 11 kawai, mun wuce adadin fasinja miliyan 41.4 da aka samu a gaba ɗaya shekarar 2024,” in ji shi.

Ministan ya ce jiragen sama 208,643 ne suka sauka ko tashi a filin jirgin saman daga watan Janairu zuwa watan Nuwamban shekarar 2023, kuma wannan adadi ya ƙaru da kaso 20 cikin 100, inda ya kai jirage 250,538 a shekarar.

Kuma ya ce a shekarar 2024 gaba ɗaya jirage 242,612 ne suka yi zirga-zirga a filin jirgin saman.