'Yanbindiga sun kashe sojojin Libya uku a kusa da kan iyakar Nijar

Dakarun gabashin Libya sun ce an kashe sojoji uku yayin da aka kama wasu a wani harin da aka kai wurin ƙetare kan iyaka na Al-Toum tsakanin Libya da Nijar.

By
Rundunar sojin gabashin Libya ta yi imanin cewa 'yan daba masu aikata laifuka da ke fasaƙurin kayayyaki sun far ma sojojinta kana suka tsere Nijar. / Reuters

An kashe sojoji uku yayin da wasu suka jikkata a wani harin da ’yanbindiga suka kai kudancin Libya kusa da kan iyakarta da Nijar, kamar yadda rundunar sojin gabashin ƙasar ta bayyana.

A wata sanarwa, rundunar sojin ta ce, an kuma kama sojoji a harin da aka kai wajen ƙetare kan iyaka na Al-Toum.

Ta ce ‘yanbindiga sun kuma far ma Wadi Bougrara da Salvador kusa da kan iyaka da Nijar.

Sanarwar ta ce ‘yanbindiga masu aikata laifuka da ke fasa-ƙaurin kayayyaki’ ne suka kai harin, tana mai ƙarawa da cewa “an samu an sake tsare” wuraren da aka kai harin inda dakarun tsaro suka bazama wuraren domin farautar maharan “waɗanda bisa ga dukkan alamu sun tsere ta Nijar.”

Daga farko wata ƙungiyar ‘yanbindiga da ke kiran kanta “‘Yan juyin-juya-hali na Kudu” ta yi iƙirarin cewa ta karɓe iko da wurin ƙetare kan iyaka na Al-Toum tsakanin Libya da Nijar.