Kotu ta ba da umarnin tsare Abubakar Malami da ɗansa a gidan yarin Kuje
Alkali Emeka Nwite ya kuma ba da umarnin a sake tsare waɗanda ake tuhuma tare da Malami wato ɗansa da kuma wata mace ma’aikaciyar kamfanin Rahamaniyya Properties, Hajiya Asabe Bashir.
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Talata ta ba da umarnin tura tare da tsare tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami (SAN), a gidan yarin Kuje har sai an kammala zaman sauraren ƙarar da kuma yanke hukunci kan buƙatar belin da ya shigar.
Alkali Emeka Nwite ya kuma ba da umarnin a sake tsare waɗanda ake tuhuma tare da Malami wato ɗansa da kuma wata mace ma’aikaciyar kamfanin Rahamaniyya Properties, Hajiya Asabe Bashir.
Tun da farko, lauyan masu gabatar da ƙara, Kelechi Ekele (SAN), ya yi adawa da bukatar belin da lauyan da ke kare Malami, Joseph Daudu (SAN) ya gabatar, a matsayin wani harin kwanton ɓauna da ba za a iya amsa shi da baki a kotu ba.
Malami da wadanda ake kara tare da shi suna fuskantar tuhume-tuhume 16 da Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Nijeriya Ta’annati (EFCC) ta shigar a kansu.
A cikin tuhumen, EFCC ta yi zargin cewa wadanda ake kara sun hada baki a lokuta daban-daban don boyewa da adana kudaden haram da suka kai biliyoyin naira.
Hukumar ta kuma yi zargin cewa laifukan, wadanda suka dauki shekaru da dama, sun hada da amfani da kamfanoni da asusun banki don wawure kudaden haram, ajiye kudi a matsayin jingina don basussuka, da kuma mallakar kadarori masu daraja a Abuja, Kano da sauran wurare.
Hukumar ta kuma yi ikirarin cewa an aikata wasu laifukan ne a lokacin da Malami ke aiki a matsayin Babban Lauyan Tarayya, sabanin tanade-tanaden Dokar Hana Zubar da Kudi ta 2011 (kamar yadda aka gyara) da Dokar Hana Zubar da Kudi ta 2022.
Duk da haka, waɗanda ake tuhuma sun musanta zargin.