Kare gaskiya na da matuƙar muhimmanci a 'zamanin labaran ƙarya': Daraktan Sadarwa na Turkiyya
Daraktan Sadarwa na Gwamnatin Turkiyya, Burhanettin Duran, ya jaddada muhimmancin kare gaskiya da yaƙi da masu “shaci-faɗi” a wannan zamani na ‘labaran ƙarya'.
Shugaban Sashen Sadarwa na Gwamnatin Turkiyya, Farfesa Burhanettin Duran, ya yi gargaɗi cewa a sabon tsarin tsaro, kare gaskiya nauyi ne da ke da matuƙar muhimmanci tamkar dai yadda kare iyakokin ƙasa yake.
“Lamarin labaran ƙarya ba batu ne kawai na sadarwa ba, yana matuƙar hatsari kai-tsaye ga tsaron ƙasa da ma duniya baki ɗaya,” in ji babban jami’in watsa labaran a ranar Jumma’a.
Da yake jawabi a wurin taron ƙasashen duniya mai taken International Strategic Communication (STRATCOM) Summit 2026 a Istanbul, ya bayyana cewa a “zamanin labaran ƙarya” ana amfani da ƙirƙirarriyar basira da algorizin na shafukan dijital domin sauya gaskiyar lamura, abin da ya zama wani makami da ke da tasiri a duniya.
“A Turkiyya, mun rungumi kare gaskiya ba kawai a matsayin zaɓi ba, sai dai a matsayin wani nauyi, a wannan zamani na ‘labaran ƙarya’,” in ji shi.
Ya jaddada buƙatar ƙarfafa “matsaya” ta yaƙi da masu “shaci-faɗi” da ke yunƙurin sauya ra’ayin al’umma game da yadda za su yi tunani nan gaba.
“Tabbatar da adalci a fannin sadarwa babban mataki ne na dawo da zaman lafiya da tsaro a duniya,” Duran ya ƙara da cewa.
Kazalika Duran ya ce fannin watsa labari ya zama wani babban makami na nuna iko, ba kawai hanyar sadarwa ko yaɗa ilimi ba.
Zamanin ‘rashin tabbas’
Shugaban sashen sadarwar ya yi gargaɗi cewa tsarin da aka samar bayan Yaƙin Duniya na II yana rushewa, inda yake samar da “rashin tabbas” tare da girgiza tsarin tafiyar da duniya.
Ya bayar da misali da abin da ke faruwa a Gaza a matsayin gazawa ta tarbiyya da tsari, yana mai cewa ƙasashen duniya sun yi shiru inda suka bari ana bayar da labari da ya fifita ɓangare ɗaya domin kawar da ƙimar ɗaya ɓangaren da kuma nuna ƙyama ga Musulmai da wariyar launin fata.
“Dokokin duniya sun gaza yin aiki a yayin da Isra’ila take yin kisan kiyashi, sannan tsarin duniya ya yi shiru a lokacin da ake kashe fararen-hula,”
Rukunin wasu ƙasashe da ke yin baki-biyu yana zubar da ƙima da kuma tarbiyyar da a baya suka yi iƙirarin karewa,” in ji Duran.
Duran ya ƙara da cewa Turkiyya, wadda ta yi fice wajen shiga tsakani da bin tafarkin diflomasiyya, tana neman warware rikice-rikice a Ukraine, Syria da Iraki, inda ƙarfin soji ya gaza yin aiki.
Ya jaddada cewa sashen yaƙi da labaran ƙarya na Turkiyya ya bankaɗo dubban labaran ƙarya tun daga shekarar 2022, sannan ya wallafa bincikensa a harsuna goma a kafofin watsa labaran gida da na ƙasashen duniya.
Duran ya yi kira da a samu wani tsari na tsarki na duniya a fannin sadarwa ta dijital, inda ya ƙara da cewa dawowa bisa labaran gaskiya shi ne ginshiƙin sake gina tsari na zaman lafiya da ƙarfin gwiwa a duniya.