Trump ya sayi takardun lamuni na aƙalla dala miliyan 82 tun daga Agustan 2025 – Bayanai

Bayanai sun nuna cewa Trump ya sayi takardun lamuni a kamfanonin da suke amfana da munfofi da tsare-tsaren gwamnatinsa waɗanda suka haɗa da kamfanin Meta, Qualcomm da JP Morgan da wasu jerin kamfanoni.

By
Mafi yawan darajar jimillar sayayyar takardun lamunin ta zarce dala miliyan 337, a cewar takardun.

Shugaban Amurka Donald Trump ya sayi takardun lamuni da suka kai na aƙalla dala miliyan 82 na kamfanoni da ƙananan hukumomi daga ƙarshen Agusta zuwa farkon Oktoba, ciki har da sabbin ɓangarorin zuba jari da ke cin gajiyar manufofinsa, in ji bayyanannun bayanan kuɗi da aka wallafa a ranar Asabar.

A cewar bayanan da Ofishin Kula da Ɗa’ar Ma’aikata na Gwamnatin Amurka ya fitar, Trump ya yi fiye da sayayya 175 ta kudi daga 28 ga Agusta har zuwa 2 ga Oktoba. Waɗannan bayyanannun bayanai, waɗanda aka yi ƙarƙashin dokar ƙeƙe da ƙeƙe ta 1978 mai suna Ethics in Government Act, ba su bayyana daidai adadin da ake kashewa kan kowace sayayya, sai dai suna kimanta kuɗin.

Mafi yawan darajar jimillar sayayyar takardun lamunin ta zarce dala miliyan 337, a cewar takardun.

Yawancin dukiyoyin da aka jera a cikin bayyanannun bayanan na ranar Asabar sun ƙunshi takardun lamuni daga hukumomi na ƙananan garuruwa, jihohi, gundumomi, sassa na makarantu da sauran hukumomi masu alaƙa da jami'an gwamnati suka bayar.

Ya haɗa da kamfanoni da dama

Sabbin zuba jarin da Trump ya yi a ɓagaren takardun lamuni sun shafi masana’antu da dama, daga ciki har da ɓangarorin da suke amfana da tsare-tsare da manufofin gwamnatinsa.

Takardun lamuni da Trump ya saya daga kamfanonin sun haɗa da kamfanonin da ke yin ‘yan hanjin kwamfuta Broadcom da Qualcomm; kamfanonin fasaha kamar Meta Platforms; da masu sayar da kayayyaki kamar Home Depot da CVS Health; da bankunan Wall Street kamar Goldman Sachs da Morgan Stanley.

Siyayya na lamunin bankunan a ƙarshen Agusta sun haɗa da a JP Morgan. A ranar Juma'a, Trump ya roƙi Ma'aikatar Shari'a ta Amurka ta binciki JP Morgan kan alaƙarta da fitaccen mai kuɗin nan wanda ake zargi da fyaɗe wato Jeffrey Epstein. Bankin ya ce yana bakin ciki game da tsohuwar alaƙarsa da Epstein kuma bai taimaka masa wajen aikata "mugayen laifuka" ba.

Har ila yau Trump ya sayi takardun lamuni daga Intel bayan gwamnatin Amurka, a ƙarƙashin umarnin Trump, ta saka hannun jari a kamfanin.

Trump ya ce kamfanoni na daban ne ke kula da kasuwancinsa

Fadar White House ba ta mayar da martani nan take ga buƙatar sharhi kan lamarin ba a ranar Asabar. Sai dai gwamnatin ta ya ce da shi da iyalansa duk ba su da hannu a kasuwancinsa inda ya ce kamfani na daban ne ke kula da kasuwancin nasa.

Trump, wanda ya samu arziki a fannin kadarorin ƙasa kafin ya shiga siyasa, ya taɓa cewa ya bayar da amanar kamfanoninsa waɗanda ‘ya’yansa ke sa ido a kai.

Wasu bayanai da aka bayyana a watan Agusta sun nuna cewa Trump ya sayi takardun lamuni na fiye da dala miliyan 100 tun dawowarsa matsayin shugaban ƙasa a ranar 20 ga Janairu. Trump ya kuma mika fom ɗin bayansa kan kadarori na shekara-shekara a watan Yuni, wanda ya nuna cewa kuɗin shiga daga fannoni daban-daban na kasuwancinsa har yanzu ƙarshe suna zuwa gare shi, abin da ya haifar da damuwa kan yiwuwar saka son rai a fannin aikinsa da kasuwanci.

A cikin waɗannan bayannanun bayanan na shekara-shekara, waɗanda suka hada da na shekarar 2024 baki ɗaya, Trump ya ce ya samu fiye da dala miliyan 600 a matsayin kudin shiga daga kirifto, filayen golf, lasisi da wasu harkokin kasuwanci. Haka kuma bayanan sun nuna cewa shigar Trump a harkar kirifto ta yi tasiri wurin ƙaruwar dukiyarsa.

Gaba ɗaya, abubuwan da Trump ya bayyana a watan Yuni na dukiyoyi da sun kai aƙalla dala biliyan 1.6, a cewar ƙididdigar Reuters a lokacin.