| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Shugaban Iran ya yi alƙawarin ba za su yi saranda ba, ya ba ƙasashe maƙwabta haƙuri
Iran ta ce ba za ta sake kai hari kan ƙasashe makwabta ba kuma ba za ta harba makami mai linzami a kansu ba sai dai idan harin da aka kai kan Iran ya fito daga ƙasashen na Gulf, in ji Shugaban Iran Masoud Pezeshkian.
Shugaban Iran ya yi alƙawarin ba za su yi saranda ba, ya ba ƙasashe maƙwabta haƙuri
Pezeshkian yana ɗaya daga cikin mutane uku na wata majalisa ta riƙon kwarya da ke shugabantar Iran bayan an kashe Khamenei. / AP
7 Maris 2026

Shugaban Iran Masoud Pezeshkian a ranar Asabar ya bayyana cewa ƙasar tasa ba za ta taɓa mika wuya ga Isra'ila da Amurka ba, yayin da yaƙin ya shiga mako na biyu.

Ya bayyana cewa, "dole ne ƙawayen Iran su tafi ƙabari da burinsu na ganin mutanen Iran sun miƙa wuya ba tare da sharadi," kamar yadda Pezeshkian ya bayyana, a cikin jawabin da aka watsa a gidan talabijin na ƙasar.

Isra'ila da Amurka sun kai farmaki kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu inda suka kashe Jagoran Addini na Iran, Ali Khamenei inda hakan ya haddasa rikici a yankin.

Tun daga lokacin, Iran ta mayar da martani da harin makami masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa a kan Isra'ila da wuraren Amurka a ƙasashen yankin na Gulf.

Pezeshkian na daga cikin mambobi uku na kwamitin shugabanci na wucin-gadi da ke jagorantar Iran tun bayan kisan Khamenei.

A lokacin jawabin, Pezeshkian ya nemi afuwa daga ƙasashen makwabta saboda hare-haren da Iran ta kai a faɗin yankin, yana mai cewa ba za a ci gaba da kai musu hare-hare ba sai dai idan hare-haren sun fito daga gare su.

"Dole ne na nemi afuwa a madadina da kuma a madadin Iran ga ƙasashen maƙwabta waɗanda Iran ta kai musu hari," in ji shi.

"Kwamitin shugabancin wucin-gadi ya yanke hukunci a jiya cewa ba za a sake kai hari kan ƙasashe makwabta ba kuma ba za a harba makami mai linzami ba sai dai idan harin da aka kai kan Iran ya fito daga wadancan ƙasashen," in ji shi.

Rumbun Labarai
Iran ta ce Amurka ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta
Iran na iya janyewa daga yarjejeniyar tsagaita wuta idan Isra'ila ta cigaba da yaƙar Lebanon: Rahoto
Sharuɗɗa 10 na zaman lafiya da Amurka ta amince da su a yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran
Mazauna Tehran sun fada halin rashin tabbas bayan barazanar Trump ta baya bayan nan
Abubuwan da ya kamata mu sani game da daftarin yarjejeniyar Amurka da Iran
Masar ta haɗa kai da Turkiyya da Pakistan don shiga tsakanin Iran da Amurka – Kafafen  Yaɗa Labarai
Amurka da Iran na duba yiwuwar cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 45: Rahoto
Amurka ta ceto direban jirgin F-15 na biyu da ake nema a Iran — Trump
Tururin nukiliya zai jawo asarar rayuka a manyan biranen ƙasashen Gulf ba Tehran ba: Araghchi
Farashin kayan abinci, man fetur da takin zamani ya ƙaru saboda yaƙin Gabas ta Tsakiya: MDD
Yadda yakin Gabas ta Tsakiya zai shafi ƙasashen Afirka a gajeren lokaci, in ji wani rahoto
Iran ta harbo jirgin yaƙin Amurka samfurin F-35
Makamai masu linzami na Iran na jarraba ƙarfin garkuwar makamai masu linzami a sararin samaniya
Iran ta ce Mashigar Teku ta Hormuz a bude take ga duniya, amma a rufe ga maƙiya
Iran ta yi ruwan makamai masu linzami kan Isra’ila bayan Trump ya yi iƙirarin daƙile ƙarfin sojinta
Isra’ila ce ummul aba'isin haramtaccen yaƙi da Iran: In ji Erdogan na Turkiyya
Kalin ya karɓi baƙuncin tawagar Hamas don tattauna shirin zaman lafiya na Gaza
Trump ya ce Amurka za ta bar Iran cikin makonni 2 zuwa 3
Iran ta ce lokaci ya yi da Saudiyya za ta kori sojojin Amurka daga yankinta
Yadda yaƙin Iran zai iya rikita kasuwancin duniya ta Mashigar Teku ta Bab al Mandeb