Ribadu ya jagoranci wata tawagar Nijeriya mai ƙarfi zuwa Amurka kan zargin kashe Kiristoci a ƙasar

Tun bayan zargin da Amurka ta yi kan kashe Kiristoci a Nijeriya, gwamnatin ƙasar ta musanta wannan zargin amma duk da haka Amurka ta ci gaba da tafiya a kan ra’ayinta kan cewa ana zaluntar Kiristoci a Nijeriya.

By
Babban Mai Bai wa Shugaban Nijeriya Shawara kan Tsaro Nuhu Ribadu

Babban Mai Bai wa Shugaban Nijeriya Shawara kan Tsaro Nuhu Ribadu ya jagoranci wata babbar tawaga zuwa Amurka kan zargin cewa ana zaluntar Kiristoci a Nijeriya.

Zargin ya ƙara karfi ne bayan Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya yi magana kan goyon bayansa ga tsarin samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu a rikicin Isra’ila da Gaza.

Tun farkon watan nan, Shugaban Amurka Donald Trump ya sake saka Nijeriya cikin jerin ƙasashen da ake sa wa ido na musamman kan walwalar addini, ya kuma bukaci wasu ‘yan majalisa, ciki har da Riley Moore su binciki halin da ake ciki a Nijeriya su dawo masa da sakamako.

Duk da kokarin da Gwamnatin Tarayya ta yi wajen fayyace gaskiya, Amurka ta ci gaba da tafiya a kan ra’ayinta kan cewa ana zaluntar Kiristoci a Nijeriya.

A ranar Talata, an gayyaci mawaƙiyar Amurka Nicki Minaj zuwa Majalisar Dinkin Duniya, MDD don ta yi ƙarin haske kan zargin zaluntar Kiristoci a Nijeriya.

Nijeriya ba ta samu damar halartar taron ba, lamarin da ya sa ta yi korafi.

Sai dai ba a ba Nijeriya damar zuwa wurin taron ba, inda Nijeriyar ta nuna rashin jin daɗinta game da wannan lamarin.

Syndoph Endoni, ƙaramin jakadan dindindin na Nijeriya a MDD, ya ce ware Nijeriya daga tattaunawar — wadda aka gudanar a hedikwatar MDD a New York — tamkar “a aske mana kai ne ba tare da mu ba.”

Taron da Minaj ta halarta an shirya shi ne tare da taimakon Wakiliyar Dindindin ta Amurka a Majalisar Dinkin Duniya.

Amma a ranar Laraba, tawagar Nijeriya ta yi bayanin ainihin halin da ake ciki a ƙasar ga ɗaya daga cikin mutanen da ke yada labarin cewa ana aikata kisan ƙare-dangi a Nijeriya.

Wadanda suka kasance cikin tawagar sun haɗa da Bianca Ojukwu, Ƙaramar Ministar Harkokin Wajen Nijeriya da Kayode Egbetokun, Sufeton ‘Yan Sanda Nijeriya da Lateef Olasunkami Fagbemi, Antoni Janar na Nijeriya da Janar Olufemi Olatunbosun Oluyede, Babban Hafsan Tsaro na Nijeriya da kuma Laftanar Janar EAP Undiendeye, Shugaban Leƙen Asiri na Rundunar Tsaron Nijeriya.