Kofin Duniya na 2026: Curacao ta zama kasa mafi kankanta da za ta buga gasar

Kasar Curacao da ke yankin Amurka ta Tsakiya tana da al'umma kimanin 150,000, da kuma faɗin ƙasa da ya kai murabba'in mil 171.

By
Curacao ta goge tarihin da Iceland ta kafa a FIFA

A karon farko a tarihinta, ƙasar Curacao ta samu damar zuwa gasar ƙwallon ƙafa ta Kofin Duniya ta FIFA 2026, wadda za a yi a ƙasashen Amurka, Canada, da Mexico a baɗi.

Ƙasar da ke yankin Amurka ta Tsakiya, ta buga wasa da Jamaica, inda suka tashi canjaras babu ci, wanda ya sa ta ƙare Rukunin B a saman teburi da maki 12 daga wasanni 6.

Curacao ƙasa ce ƙarama wadda al'ummar suka kai kimanin 150,000, da kuma faɗin ƙasa da ya kai murabba'in mil 171.

A yankin hukumar ƙwallo ta CONCACAF da ke Amurka ta Tsakiya, Curacao da Haiti da Panama ne suka samu cancantar zuwa yanzu.

Zuwan Curacao, na nufin cewa ta goge tarihin da Iceland ta kafa na zama ƙasa mafi ƙanƙanta da ta buga gasar, inda ta je gasar da aka yi a Rasha a 2018.

Daraja a FIFA

A yanzu dai Curacao ce ƙasa ta huɗu da za ta buga gasar ta baɗi a karon farko, baya ga Cape Verde, Jordan, da Uzbekistan.

A 2010 ne Curacao ta zama ƙasa wadda ke cikin daular Masarautar Netherlands, sakamakon kawo ƙarshen tsarin yankin Netherlands Antilles.

A yanzu haka, ƙasar na da daraja ta 82 a jerin ƙasashen duniya mambobin FIFA.

Ita kuwa Jamaica ta zo ta biyu a rukunin, kuma za ta ci gaba da gwada sa’arta a wasannin cike gurbi da za a yi Mexico.

Kocin Jamaica, Steve McClaren wanda tsohon kocin Ingila ne kuma tsohon mataimakin kocin Manchester United, ya ajiye aiki nan-take, bayan gazawar ƙasar.