Rundunar sojin saman Nijeriya ta ce ta fara bincike kan wasu rahotanni da ke cewa an samu mace-macen fararen-hula da yawa yayin hare-haren sama da ta kai kasuwar Jilli kusa da ƙauyen Fuchimiram a ƙaramar hukumar Geidam ta jihar Yobe, a arewa maso gabashin ƙasar.
Ranar Lahadi ne dai rundunar sojin ƙasar ta fitar da sanarwar kai hari Jilli inda ta wallafa hotuna na harin da suka nuna ababen da ta kira motocin ‘yanta’adda da ma sauran kayan yaƙi da ta kai wa hari a kasuwar.
Sai dai kuma yayin da rundunar sojin saman ta Nijriya ta ce ta yi nasarar kai hari kan wurin da ta kira cibiyar kasuwancin 'yanta'addaa a arewa maso gabashin ƙasar, wasu rahotanni na cewa kimanin fararen-hula 200 aka kashe a harin.
A sanarwar da ya fitar, daraktan watsa labaran rundunar sojin saman Nijeriya, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce rundunar “tana ɗaukar duk rahotannin yiwuwar jikkata fararen-hula a matsayin abin damuwa sosai da kuma abin tausayi”.
“Bisa ga wannan rahoto, babban hafsan sojin sama ya ba da umarnin tura wata tawaga domin yin bincike kan zargin,” in ji sanarwar.
“Hari kan ‘yanta’adda”
A wata sanarwa da ta fitar tun da farko, rundunar sojin saman Nijeriya ta tabbatar da kai hare-haren sama a yankin Jilli amma ba ta bayyana ko an samu mutuwar fararen-hula ba.
An kai hare-haren ne “yayin da muke zafafa ƙoƙarin nemo da kassara ‘yanta’addan da suka kai hari kwanan baya kan dakarun tsaro a fagen yaƙin, kuma an ƙaddamar da hare-haren ne kan [‘yanta’adda] masu tserewa domin ƙara haɗuwa a wani wurii,” in ji rundunar sojin saman Nijeriya.
Hari ranar kasuwa
Hukumomi da mazauna yankin sun tabbatar da aukuwar harin da suka ce ya faru ne daidai lokacin da ake tsaka da gudanar da harkokin kasuwanci.
Gidan talbijin na Channels ya ruwaito cewa wani ganau ya tura masa hotuna daga babban asibitin ƙwararru na Geidam inda ya ce da yawa daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su suna karɓar magani.
Sai dai kuma gidan talbijin ɗin ya ambato wata majiya a yankin da ke cewa harin ya faru ne yayin da wani jirgin yaƙin Nijeriya ke bibiyar tafiyar wasu ‘yan Boko Haran waɗanda rahotanni suka ce sun je karɓar haraji ne daga mazauna yankin kafin jirgin ya kai harin.
Gwamnatin jihar Yobe ta bayyana cewa an kai harin ne kan ‘yan Boko Haram.
Rufe kasuwa shekaru 5 da suka wuce
Kazalika gwamnatin jihar Borno ta ce an rufe kasuwar shekaru biyar da suka wuce sakamakon yadda ‘yanta’adda ke amfani da ita a matsayin wurin sayen kayan amfanin yau da gobe.
Wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan watsa labarai, Dauda Iliya, ya fitar ta ce gwamnan jihar da na jihar Yobe suna tuntuɓar juna da rundunar soji game da harin.
















