| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Tashin farashin mai a Nijeriya ya yi ƙamari yayin da yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran ya ƙi ƙarewa
Tashin farashin man yana ƙara tsadar rayuwa tare da rage wa wasu mutane kuɗin shiga a ƙasar ta Yammacin Afirka.
Tashin farashin mai a Nijeriya ya yi ƙamari yayin da yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran ya ƙi ƙarewa
Tashin farashin man fetur a Nijeriya na tsananta tsadar rayuwa tare da rage wa wasu mutane kuɗaɗe shiga / Reuters
23 Maris 2026

Yayin da yaƙin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar kan Iran ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, farashin fetur a Nijeriya na ƙaruwa babu ƙaƙƙautawa zuwa kusan N1,400 kan ko wace litar mai lamarin da ke tayar da hankalin matafiya da ‘yankasuwa da direbobi, a cewar jaridar Daily Trust.

Rahotanni daga Nijeriya sun nuna cewa tashin farashin na baya bayan nan, wanda ya samo asali daga tashin farashin ɗanyen mai wanda kuma yaƙin Iran ne sanadinsa, yana rage kuɗaɗen shigar mutane da ƙara tsadar kuɗin mota tare da tsananta tsadar rayuwa ga miliyoyin ‘yan Nijeriya.

Yayin da farashin gangar ɗanyen mai ya kai kusan $120 a makon jiya kafin ya tsaya a $112 ƙarshen mako sannan rikicin Gabas Ta Tsakiya ke ci gaba, matatar man Dangote ta ƙara farashin manta daga N1,175 zuwa N1,245 kan ko wane litar man fetur.

Sakamakon ƙarin na baya bayan nan, ‘yankasuwa ma sun sauya farashin mansu a faɗin ƙasar inda suka mayar da farashin lita ɗaya na man fetur zuwa N1,310, N1,325, N1,370 ko kuma N1,400 bisa wurin da ake sayar da man.

A Legas, direbobin motocin fasinja sun ce tashin gauron zabin farashin man yana laƙume ribarsu tare da barazana ga hanyar samunsu. A gidajen mai da dama farashin mai ya yi ta sauyawa ne tsakanin N1,320 zuwa N1,330 a kan ko wace litar mai a ƙarshen mako, inda wasu gidajen mai suka sayar da man kan N1,380 ga lita kafin su saukar da farashin, in ji Daily Trust.

A gidajen man kamfanin mai na ƙasar (NNPCL), an sauya farashin mai sau biyu a cikin ‘yan kwanaki, lamari da ya nuna rashin tabbas da ke ɓangaren tacewa da sayar da tataccen mai na ƙasar.

Jaridar ta ambato Toheeb Sulaimon, wani direba da ke jigilar matafiya a hanyar Ogba zuwa Ikeja a birnin Legas, yana cewa kuɗaɗen da yake samu a yini sun ragu sosai sakamakon ƙarin tsadar man fetur da kuma raguwar yawan mutane masu hawa mota.

“A lokacin da ake sayar da mai kan N800 ga ko wace lita, nakan iya kashe kimanin N9,000 kan mai kuma na iya samun kuɗi N30,000 a ko wace rana. A halin yanzu, komai ya canza. Kudin ya ruɓanya, amma fasinjoji sun ragu,” kamar yadda ya shaida wa Daily Trust.

Maduka Chibo, wani direban na daban, ya ce kuɗin da yake kashewa a kan mai ya ƙaru sosai zuwa N20,000, idan aka kwatanta da kimanin N10,000 da yake kashewa a lokacin da ake sayar da fetur kan N800 ga lita.

Farashi ya kai N1,390 a biranen arewacin ƙasar

A Kano, farashin man fetur ya kai har N1,390 ga ko wane lita, inda wasu ‘yankasuwa ke ƙara kuɗin mansu bisa tsadar kuɗin sayowa.

Tashoshin mai irin su AA Rano da sauransu sun mayar da farashin man su daga kimanin N1,330 zuwa tsakanin N1,385 zuwa N1,390.

Ƙarin ya haddasa tasiri mai yawa kan harkar sufuri inda masu A-Daidaidata-Sahu suka ƙara farashin jigilarsu sosai.

Wani mazaunin birnin, Ismail Mabo, ya ce an caje shi N4,000 kan tafiyar da a da za a caje shi kimanin N1,000 ne kawai, inda ya zargi masu A-Daidaidata-Sahun da amfani da yanayin a matsayin damar tsanantawa domin samun riba mai yawa.

Wani mazaunin birnin, Abba Kabir, kuwa gargaɗi ya yi cewa ci gaba da tashin farashin man zai sa masu motoci da yawa su ajiye motocinsu .

“Idan aka ci gaba a haka, mutane za su dena amfani da motocinsu. Wasu ma za su iya mayar da su kabu-kabu domin su samu biyan buƙata,” in ji shi.