MDD ta yi gargaɗin cewa yaƙin Sudan na gurgunta tattalin arzikin Sudan ta Kudu

"Yaƙin Sudan na ci gaba da shafar yanayin tsaro a Sudan ta Kudu inda ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai ke zirga-zirga a kan iyakokinta," a cewar wani babban jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya

By
Rikicin Sudan yana shafar tattalin arzikin Sudan ta Kudu, kan yana ƙara ta'azzara matsalar rashin tsaro: Majalisar Dinkin Duniya

Wani babban jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya ya faɗa a ranar Laraba cewa yaƙin Sudan ya haifar da cikas ga zaman lafiyar Sudan ta Kudu tare da ta'azzara yanayin taɓarɓarewar tattalin arziki da jinƙai a kan iyakokin da suka haɗa ƙasashen biyu.

"Yaƙin da aka soma tun daga watan Afrilun 2023 tsakanin Sojojin Sudan (SAF) da Rundunar kai Ɗaukin Gaggawa (RSF) na ci gaba da shafar dangantakar da ke tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu," kamar yadda Guang Cong, mataimakin wakili na musamman ga babban sakataren tawagar MDD a Sudan ta Kudu (UNMISS) ya shaida wa kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.

"Yaƙin Sudan na ci gaba da shafar yanayin tsaro a Sudan ta Kudu inda ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai ke zirga-zirga a kan iyakoki da kuma kewayensu," in ji shi.

Ya yi gargaɗin cewa lamarin na ƙara ta'azzara yanayin taɓarɓarewar tattalin arzikin Sudan ta Kudu mai rauni, lamarin da ya haifar da raguwar tattalin arzikin ƙasar da kashi 24.5 cikin 100.

Ya kuma bayyana cewa "hare-haren da RSF ta kai a wuraren man fetur, musamman hare-harenta da jiragen sama marasa matuƙi a kan tashar man fetur na Sudan ta Kudu a Port Sudan a ranakun 5 da 6 ga watan Mayu, da kuma wani hari na ranar 26 ga Agusta kan wuraren mai a Heglig, kusa da kan iyakar Sudan da Sudan ta Kudu sun haifar da kwararar mai tare da lalata muhalli wanda ya sa aka dakatar da ayyuka cikin gaggawa."

Yankin Abyei mai arzikin mai yana ƙarkashin ikon Sudan ta Kudu da Sudan, inda dukkan ɓangarorin ke da kaso a ciki kuma suna fama da tashe-tashen hankula na tsawon shekaru.

Ya ƙara da cewa "kimanin mutane 41,000 da suka rasa matsugunansu a Sudan sun shiga yankin Abyei tun lokacin da aka soma yaƙi a Sudan, wanda hakan ya sanya matsin mai tsanani kan ƙarancin ruwa, abinci, kiwon lafiya, matsugunai da sauran albarkatun jinƙai waɗanda dama ana fama da ƙarancinsu."

Dangane da batun yanayin tsaro, Cong ya ce Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da nuna damuwa game da "ƙaruwar kasancewar hare-haren RSF a arewacin Abyei wanda hakan ya saɓa wa Yarjejeniyar 2011 kan Shirye-shiryen Wucin-Gadi da kuma ƙudurorin Majalisar Tsaro kan iyakar Abyei."

Martha Ama Akyaa Pobee, mataimakiyar sakatare janar na Afirka a sashen harkokin siyasa da na zaman lafiya, ta ce "tsarin siyasa tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu kan yankin Abyei da kuma batutuwan da suka shafi kan iyakoki sun tsaya cak" saboda tashe-tashen hankula.

Ta kuma ƙara da cewa ‘‘kasancewar ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai, ciki har da rundunar RSF, ya haifar da kafa shingayen bincike ba bisa ƙa’ida ba a arewacin Abyei,’’ lamarin da ya tilasta rundunar samar da zaman lafiya ta MDD shiga tsakani.

‘‘Ina jaddada kiran gaggauta janye dukkan sojoji da sauran masu ɗauke da makamai daga Abyei, bisa ga yarjejeniyar hana makamai ta Abyei," in ji Pobee, tana mai ƙari da cewa majalisar na ci gaba da tallafa wa abokan hulɗa a aikin jinƙai don shawo kan "matsalar rashin abinci mai gina jiki a tsakanin yara."

Pobee ta ce, rage kasafin kuɗin UNISFA da kashi 15 cikin 100 "zai yi matukar tasiri ga ƙarfin gwiwar aiwatar da aikin da aka sa a gaba wajen rage yawan sojoji da ma’aikata fararen-hula" da kuma taƙaita muhimman ayyukan tallafi.