Matatar man Dangote za ta buɗe sayar da hannayen-jarinta na farko ga jama’a (IPO) ranar Litinin, lamarin da zai bai wa masu zuba jari damar mallakar wani kaso a matatar mai mafi girma a Afirka.
Za a ƙaddamar da hannayen-jarin a yau Litinin 14 ga Satumban 2026, a hukumance a wani biki da za a gudanar a zauren hannun-jari na Kasuwar Hannun-Jari ta Nijeriya (NGX) da ke jihar Legas.
Matakin zai bai wa jama'a damar mallakar hannun-jari a babban matatar mai na Afirka wanda kuma ke zama ɗaya daga cikin manyan masana'antu masu matuƙar muhimmanci a duniya, hannun-jarin, ya ƙunshi sabbin hannayen-jari biliyan 4.1, inda za a sayar da kowanne kan Naira 525.
Mafi ƙanƙantar adadin da mutum zai iya saya shi ne hannun-jari 10, wanda ya kai Naira 5,250. Kana ana sa ran za a rufe tayin sayar da hannayen-jarin a ranar 13 ga watan Oktoba, bisa sharuɗɗan da ke cikin takardar bayanin tayin.

Kazalika ana sa ran hannayen jarin matatar (IPO) zai tara kusan Naira tiriliyan 2.15, adadin da ake ganin zai kasance cikin manyan hannayen jari da aka taɓa sayarwa a Afirka.
Kamfanin Dangote ya ce za a yi amfani da kuɗin wajen faɗaɗa ayyukan matatar, tare da gudanar da wasu manyan tsare-tsare da kuma zuba jari a ayyukan da za su taimaka wajen bunƙasa kamfanin.
Shugaban rukunin Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa sayar da hannayen jarin wani mataki ne na bai wa ’yan Nijeriya da ’yan Afirka da sauran masu zuba jari dama a ci gaba da kuma bunƙasar matatar.
A nasa bangaren, Shugaban Hukumar Gudanarwar na Kasuwar Hannun Jari ta Nijeriya (NGX), Temi Popoola, ya ce tayin hannayen jarin zai iya ƙara yawan ’yan Nijeriya da ke shiga kasuwar hannayen jari, tare da bai wa jama’a damar cin gajiyar ci gaban manyan kamfanonin cikin gida.
Masu son sayen hannayen-jarin za su iya yin hakan ta hanyoyin da aka amince da su, ciki har da NGX Invest da bankunan kasuwanci da dillalan hannayen-jari, bisa tanadin da ke cikin tsarin tayin hannayen-jarin.
Tun bayan fara gudanar da ayyukanta na kasuwanci, matatar Dangote ta samar da man fetur da sauran kayayyakin man fetur ga kasuwannin Nijeriya da na ƙasashen waje.
A halin yanzu Matatar na samar da man fetur da ya kai ganga 700,000 a kowace rana, wanda ya zarce adadin ganga 650,000 da aka tsara za ta iya samarwa tun farko.
Kamfanin ya ce matatar na taimakawa wajen rage dogaro da man da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje, da kuma rage fitar da kuɗaɗen waje, yayin da take ƙara wa Nijeriya damar zama babbar mai fitar da kayayyakin man fetur zuwa ƙasashen waje.


















