Shugaban Hukumar Ƙwallo Ƙafa ta Duniya (FIFA) Gianni Infantino ya goyi bayan wani ƙuduri mai cike da ce-ce-ku-ce na shigar da masu zuba jari masu zaman kansu cikin wani sabon rukunin kasuwanci da zai kula da shirye-shiryen gasanni na hukumar da kuma harkokin kasuwancinta, yana mai bayyani shi a matsayin wata "dama ta musamman" don hanzarta ci-gaban kwallon ƙafa a faɗin duniya.
Tun bayan gabatar da shirin a ranar Talata Infantino yake ta shan suka, inda masu adawa da shi suka yi gargaɗin cewa zai iya bai wa masu zuba jari masu zaman kansu dama mai ƙarfi da tasiri a gasannin hukumar FIFA, ciki har da gasar Kofin Duniya.
"Shirin FIFA Forward Enterprise, ko FFE, a zahiri shawara ce, kuma tayi ne. Yana cikin tsarin dimokuraɗiyya da tsarin shawarwari, sannan a takaice, dama ce, ba wajibi ba," in ji Infantino a cikin wani bidiyo da aka fitar a ranar Laraba da yamma.
"Dama ce ta musamman don ƙara ƙarfin ci-gaban wasannin FIFA a duniya. Kamar yadda na ce tayi ne kawai, ba wajibi ba."
Tsarin kasuwanci
A ƙarƙashin ƙudurin, FIFA Forward Enterprise zai ƙarfafa hakkokin kasuwanci na FIFA, gami da watsa shirye-shirye da ɗaukar nauyi da sayar tikitin kallon wasanni da kuma lasisi, tare da shirya gasa.
FIFA na shirin tara dala biliyan 4.2 ta hanyar sayar da tsirarun hannayen-jari ga ‘yan kasuwa masu zaman kansu, wanda a farko aka kimanta zai kai dala biliyan 20.
Hukumar gudanarwa ta FIFA ta ce za ta ci gaba da iko kan FFE da kuma iko na musamman kan dokokin ƙwallon ƙafa da shirye-shiryen gasanni da kuma kalandar wasannin ƙasa da ƙasa.
Infantino ya ce shirin ya ƙuduri aniyar buɗe “darajar kasuwanci da a baya ba a mayar da hankali a kai ba” kuma zai buƙaci goyon bayan mafi yawan mambobin ƙungiyoyin FIFA 211 da kuma amincewa daga Majalisar FIFA.
Sai dai ƙudurin ya jawo suka mai zafi kan sahihanci da shugabanci da kuma yiwuwar tallatar da gasar Kofin Duniya.
A cewar UEFA “ruhi da shugabanci” na ƙwallon ƙafa ba kadarorin da za a yi kasuwancinsu ba ne, tana mai ƙari da cewa “ba alhakin FIFA ba ne ya sayar.”
Infantino ya yi watsi da shawarwarin cewa tsarin saka hannun jarin zai canza ƙa’idojin gasar sosai, yana mai jaddada cewa magoya baya za su amfana daga ƙarin kuɗaɗe a ƙasashensu.
















