Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ta bayyana shirinta na ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙasar Masar wajen yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi da shaye-shaye ta hanyar rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna (MoU).
Yarjejeniyar za ta mayar da hankali kan musayar bayanan sirri, gudanar da ayyukan haɗin gwiwa da kuma horas da jami'an hukumomin yaƙi da miyagun ƙwayoyi na ƙasashen biyu.
Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ne ya bayyana hakan a Abuja yayin da Jakadan Masar a Nijeriya, Mohammed Fouad, ya kai masa ziyarar ban girma a ranar Talata.
Marwa ya ce matsalar fataucin miyagun ƙwayoyi ta zama ƙalubale na duniya, wanda ya sa ya zama dole ƙasashe su haɗa ƙarfi domin dakile ayyukan ƙungiyoyin masu safarar ƙwayoyi.
Ya ce yarjejeniyar da ake shirin kulla da Masar za ta ƙara ƙarfafa kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu tare da bunƙasa haɗin gwiwa wajen yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi a nahiyar Afirka.
A cewarsa, NDLEA na aiki tare da hukumomin yaƙi da miyagun ƙwayoyi na ƙasashe da dama, ciki har da Amurka, Birtaniya, Faransa, Jamus da Indiya.
Da yake bayyana wasu daga cikin nasarorin da hukumar ta samu kwanan nan, Marwa ya ce NDLEA ta rushe dakunan ƙera sinadarin methamphetamine guda biyu da ake zargin wasu 'yan ƙungiyoyin fataucin miyagun ƙwayoyi daga Mexico ke gudanarwa a Nijeriya.
Ya ce ɗaya daga cikin dakunan ƙerar an kiyasta darajarsa ta kai dala miliyan 362.
Ya ƙara da cewa irin waɗannan nasarori sun nuna muhimmancin haɗin kan ƙasashen Afirka domin hana ƙungiyoyin masu safarar miyagun ƙwayoyi na ƙasa da ƙasa faɗaɗa ayyukansu a nahiyar.
A nasa jawabin, Jakadan Masar a Nijeriya, Mohammed Fouad, ya ce ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Nijeriya da Masar na da matuƙar muhimmanci wajen tinkarar matsalar fataucin miyagun ƙwayoyi.
Ya bayyana cewa ziyararsa ta mayar da hankali ne kan tattauna hanyoyin da ƙasashen biyu za su yi aiki tare domin yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin da ke da alhakin wannan aiki.
Ana sa ran yarjejeniyar fahimtar juna da ake shirin sanyawa hannu za ta samar da ingantaccen tsari na haɗin gwiwa tsakanin Nijeriya da Masar wajen yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi da kuma shaye-shaye.

















