Abin da ya sa Kungiyar Tuntuba ta Arewa ta ce Nijeriya ta shiga yanayi na yaƙi
NIJERIYA
5 minti karatu
Abin da ya sa Kungiyar Tuntuba ta Arewa ta ce Nijeriya ta shiga yanayi na yaƙiWannan matsayi na ACF yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fitar bayan kammala taron kwamitin amintattu na kungiyar karo na 38 da aka gudanar a Abuja.
Nijeriya na fama da hare-haren ta'addanci daga kungiyoyi daban-daban. / Reuters
4 awanni baya

Da alama matalsar da ta daɗe tana addabar Nijeriya musamman yankin arewaci ta kai magaryar tuƙewa bayan da Kungiyar Tuntuba ta Arewa (Arewa Consultative Forum - ACF) ta bayyana halin da ake ciki a kasar da yanayin yaƙi saboda yadda ake ci gaba da samun taɓarɓarewar tsaro a sassa daban-daban na kasar.

Da farko dai murnar da ’yan kasar suke yi dangane da saukin da aka samu ta fuskar hare-haren Boko Haram ta fara komawa ciki saboda a ’yan watannin nan an ga sabbin hare-haren kungiyar musamman a Jihar Borno.

Kuma a hare-haren kungiyar na baya bayan nan ya haɗa har da manyan jami’an sojin kasar ciki har da masu riƙe mukamin janar-janar, wadanda suka rasa rayukansu a bakin daga a kokarinsu na kare kasar da al'ummarta.

Wannan matsayi na ACF yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fitar bayan kammala taron kwamitin amintattu na kungiyar karo na 38 da aka gudanar a Abuja.

A cikin sanarwar, ƙungiyar ta bayyana cewa ƙalubalen tsaron Nijeriya—tun daga tayar da ƙayar baya a Arewa maso Gabas, da garkuwa da mutane a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, da kuma rikice-rikicen kabilanci da suka ƙi ci, suka ƙi cinyewa—sun rincaɓe zuwa babban rikici da ke barazana ga zaman lafiyar ƙasa baki ɗaya.

Sakamakon wadannan matsaloli ne Ƙungiyar ACF ta yi gargaɗin cewa tabarbarewar tsaro a Nijeriya ya kai matakin da za a iya bayyana shi a matsayin “yanayin yaƙi,” inda ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakan gaggawa na musamman don magance wannan matsala.

Malam Bashir Dalhatu ne ya jagoranci taron, wanda ya sami halartar jiga-jigan yankin arewacin kasar, ciki har da tsohon Sufeto Janar na ’Yansanda, Mohammed Abubakar da tsohon Shugaban Hafsan Sojin Ƙasa, Tukur Buratai da tsohon Shugaban Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya UNGA, Tijjani Muhammad-Bande da sauransu.

Haka kuma, ACF ta yi gargaɗin cewa girman wannan matsala da yadda take ci gaba, da kuma asarar rayukan da ake samu, na buƙatar sauyi na gaske a kan abubuwan da ƙasa ta sa gaba a wannan lokaci. Kazalika ta jaddada cewa dole ne a ɗauki wannan batu a matsayin wani muhimmi na gaggawa da gwamnatocin kasar gaba daya za su mayar da hankalin a kai (wato National Emergency).


Shi ma masani kan al’amuran da suka shafi tsaro Dokta Kabiru Adamu a baya ya taɓa shaida wa TRT Afrika Hausa cewa kowane mizani ka dauka za ka ga cewa Nijeriya tana da rauni ta fuskar tsaron kasa.

 Dokta Kabiru ya bayar da misalin cewa mutum fiye da 10,000 ne suka mutu a Nijeriya a shekarar 2025 sanadin matsalar tsaro.

Ya ce yana da wuya ka samu wata kasa a duniya wacce aka kashe mutane haka da yawa a shekara daya saboda matsalar tsaro, kuma a ce kasar ba a cikin yaƙi take ba tsundum, yana mai cewa Nijeriya ce kasa ta biyar a duniya da ta fi fama da rashin tsaro.

Duk da cewa babu wata hukuma ko kungiya mai zaman kanta a Nijeriya ko ta duniya da ta ce Nijeriyar ta shiga yanayin yaƙi kamar yadda ACF ta bayyana a yanzu, a baya bayanai sun sha nuna cewa kasar na daga gaba-gaba a duniya wajen yawan mutanen da ake kashewa alhali ba a yanayi na yaƙi take ba.

Wata ƙungiya ta Global Burden of Armed Violence da ke rarrabe yawan mace-macen da ake samu a duniya a bisa rukunin yaƙi da wadanda ba na yaƙi ba, ta ce tun shekarar 2011 Nijeriya ke yawan fitowa a jerin kasashen da ake samun mutuwar mutane da yawa alhali ba yaƙi take yi ba.

Ita ma Mujallar Lafiya ta Lancet a wata maƙalarta a watan Yunin 2025 ta ce yanayin da ake ciki a Nijeriya ya kai matakin da tabarbarewar lafiyar jama'a ke bukatar daukin gaggawa kuma ya zama barazana sosai ga zaman lafiya wanda ya sha bamban da wanda aka saba gani a yaƙi na yau da gobe.

Masana harkokin tsaro ciki har da Malam Kabiru Adamu suna ganin saboda wannan tabarbarewar tsaron ne ya sa a farkon wannan shekara gwamnatin Nijeriya ta gayyato Amurka don ta dafa mata wajen magance matsalar, musamman bayan da Amurkan ta yi kurarin far wa Nijeriya saboda zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi, lamarin da gwamnatin Nijeriyar da ma masu sharhi a ciki da wajen kasar suka ce ba wani addini guda yake shafa ba, abu ne da ke shafar kowane bangare.

Sai dai kuma kimanin watanni biyu bayan isar dakarun Amurka kasar bisa sharaɗin taimakawa wajen daƙile rashin tsaron, ‘yan ƙasar da dama na ganin matsalar ƙara taɓarɓarewa take yi.

Yayin da sojojin kasar suke cewa suna samun nasarori wajen kawar da manyan kwamandoji, Dokta Kabiru Adamu ya ce wannan ba ya haifar da zaman lafiya mai ɗorewa na dogon lokaci.

Ya ce gwamnati tana kashe kwamandojin ‘yanta’adda, amma ba ta iya hana su daukar sabbin mambobi. Saboda haka masanin tsaron ya ce 'yanta'addar suna sake farfadowa da sake fasalinsu.

Masanin tsaron ya ce mafita ita ce har sai gwamnati ta katse hanyoyin daukar sabbin mambobi a kungiyoyin 'yanta'adda - wanda galibi talauci da aƙida, da matsalolin cikin kasa ke sanya su shiga– idan ba haka ba za a dauki lokaci mai tsawo ba a magance wadannan matsalolin tsaron ba.