Gwamnatin Nijeriya ta ba da umarnin soke fasfo ɗin mutanen da suka janye daga kasancewa ’yan ƙasar

Wannan umarni ya shafi ’yan Nijeriya da Shugaban Ƙasa ya amince da buƙatarsu ta janyewa daga kasancewa ’yan ƙasa.

By
Wannan umarni ya shafi ’yan Nijeriya da Shugaban Ƙasa ya amince da buƙatarsu ta janyewa daga kasancewa ’yan ƙasa. / TRT Afrika English

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya umarci Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) da ta gaggauta soke fasfo ɗin mutanen da suka bayyana janyewarsu daga zama ’yan ƙasar a hukumance.

Wannan umarni, wanda ke ƙunshe cikin wata sanarwa da Mashawarcin Ministan kan Harkokin Yaɗa Labarai, Alao Babatunde, ya fitar ranar Asabar, ya shafi ’yan Nijeriya da Shugaban Ƙasa ya amince da buƙatarsu ta janyewa daga kasancewa ’yan ƙasa.

Tunji-Ojo ya bayyana cewa ma’aikatar, wadda ke da alhakin kare mutuncin zama ɗan kasa, ta samu hurumin bayar da wannan umarni ne daga Sashe na 29(1) da (2) na Kundin Tsarin Mulkin Ƙasar na shekarar 1999 (wanda aka gyara).

Sanarwar ta ce tanadin kundin tsarin mulkin yana cewa: “(1) Duk wani ɗan ƙasar Nijeriya da ya kai munzalin balaga, wanda yake buƙatar janye kasancewarsa daga zama ɗan ƙasar Nijeriya, zai bayyana hakan ne ta hanyar da aka tsara don yin hakan.

“(2) Shugaban Ƙasa zai sa a yi rajistar wannan bayanin murabus da aka yi a ƙarƙashin ƙaramin sashe na (1) na wannan sashe, kuma bayan an yi rajistar, mutumin da ya bayyana janyewarsa din zai daina zama ɗan ƙasar Nijeriya.”

A cewar sanarwar, ministan ya ce da zarar mutum ya daina zama ɗan ƙasa, ba shi da hurumin ci gaba da riƙe ko waɗanne irin takardun ikon ƙasa na Nijeriya, ciki har da fasfo.

Haka kuma, ya bayyana wannan mataki a matsayin wanda ya yi daidai da gyare-gyaren da ma’aikatar ke gudanarwa kan harkokin fasfo da biza a shekarun baya-bayan nan.

Ya ce sabon umarnin na nufin toshe hanyar da ke bai wa tsofaffin ’yan ƙasa damar ci gaba da amfani da fasfon Nijeriya wajen tafiye-tafiye ko da bayan an amince da janye su ɗin a hukumance.

“Za mu ci gaba da ƙarfafa tsare-tsaren da ke tsare iyakokin Nijeriya, hana zambar su ko yin takardun bogi, kare alfarma da mutuncin zama ɗan ƙasar Nijeriya, da kuma sauƙaƙa tafiye-tafiye na hanyar bin ƙa’ida yayin da muke hana waɗanda ba su da hurumi samun dama,” in ji Tunji-Ojo.