Zaman lafiyar Iran na da muhimmanci ga tsaron yankin: Turkiyya

Ankara ta ce za ta ci gaba da kokarin ganin an kai kayan taimakon jinkai zuwa Gaza, tana sake tabbatar da shirin Turkiyya na daukar nauyin sake gina Gaza.

By
Turkiyya za ta ci gaba da kokarin kawo karshen yakin Rasha da Ukraine. / x

Majalisar Tsaron Ƙasa ta Turkiyya ta tattauna kan al’amuran da ke faruwa a yankin, tana mai jaddada cewa kwanciyar hankali a maƙwabciyarta Iran yana da matuƙar muhimmanci ga tsaron yankin, kamar yadda ta kuma yi bitar yanayin da ake ciki a Gaza, Syria da Ukraine, a cewar wata sanarwa da aka fitar.

Majalisar, wacce Shugaba Recep Tayyip Erdogan ke jagoranta, ta ce a ranar Laraba cewa an tattauna abubuwan da suka faru kwanan nan da suka shafi Iran dalla-dalla, inda ta jaddada cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali a Iran suna da "muhimmanci" ga tsaron yankin baki ɗaya.

Taron ya kuma yi bitar yanayin da ake ciki a Gaza da kuma makomar tsagaita wuta, inda ta sake tabbatar da shirin Turkiyya na ɗaukar alhakin sake gina Gaza da kuma kafa zaman lafiya mai ɗorewa tare da haɗin gwiwar abokan hulɗarta.

Ankara ta ce za ta ci gaba da ƙoƙarin isar da cikakken tallafin jinkai ga Gaza, tana mai jaddada cewa a shirye take ta ɗauki dukkan nauyin da ke kanta don sake gina Gaza da kuma assasa zaman lafiya mai ɗorewa.

Majalisar ta sake jaddada goyon bayanta ga ikon mallakar Syria da kasar ke da shi, mutuncin iyakokinta, tsarin haɗin kan siyasa, yayin da ta yi alƙawarin ci gaba da ƙoƙarin da aka yi na inganta tsaro, kwanciyar hankali da samun wadata ga al'ummar Syria.

Yaki da ta’addanci

An sake duba yakin da Turkiyya ke yi da ta'addanci, ciki har da PKK/KCK-PYD/YPG, FETO da Daesh, inda majalisar ta sake jaddada kudirinta na dakile barazanar da ke tattare da hadin kan kasa da tsaro a cikin gida da kuma kasashen waje.

Majalisar ta tantance ci gaban da aka samu a karkashin manufar "Turkiyya Marsr Ta'addanci", tana mai cewa matakan karfafa tsaro, kwanciyar hankali da wadata a kasar da yankin za su ci gaba da dorewa.

An kuma jaddada goyon bayan 'yancin kai da kuma 'yancin yankunan Somalia, inda Turkiyya ta sake jaddada kudirinta na tsayawa tare da al'ummar Somalia a yakin da suke yi da kungiyoyin ta'addanci.

Taron ya ƙara yin nazari kan yakin da ake yi a Ukraine, yana mai gargadin cewa illar da hakan zai haifar ba za ta kawo cikas ga kokarin kiyaye zaman lafiya a cikin Tekun Baharul Aswad ba, tare da yin kira ga dukkan bangarorin da su dauki mataki mai kyau.

Turkiyya ta ce za ta ci gaba da kokarin taimakawa wajen kawo karshen yakin da kuma cim ma zaman lafiya mai dorewa.

Majalisar ta kuma yi nazari kan ci gaban siyasa, soja, tattalin arziki da zamantakewa a shekarar 2025 wanda ke da tasiri ga tsaron ƙasa kuma ta tattauna kan hatsarin da ka iya taso wa da kuma matakan da za a ɗauka a shekarar 2026.

Ta kammala da cewa Turkiyya za ta ci gaba da ƙoƙarinta na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin duniya baki ɗaya, tun daga maƙwabtanta zuwa Asiya, Afirka da Turai.