Hamas ta ce an kashe masu leƙen asirin Isra’ila huɗu a arewacin Gaza

Masu leƙen asiri sun yi ƙoƙarin garkuwa da wani ɗan Hamas a Gaza, kamar yadda dakarun Qassam suka yi iƙirari.

By
Hamas ta ce masu leƙen asirin Isra’ila huɗu ne aka kashe a arewacin Gaza / AA

Hamas ta bayyana ranar Litinin cewa an kashe mutum huɗu da ke yi wa Isra’ila leƙen asiri a arewacin Gaza.

“An kashe masu leƙen asiri huɗu waɗanda ke yi wa abokiyar gaba Isra’ila aiki kuma suka yi ƙoƙarin yin garkuwa da wani ɗan Hamas a Gaza,” in ji ɓangaren sojin ƙungiyar, Qassam Brigades, a cikin wata sanarwa a kafarta ta manhajar Telegram.

Qassam ta ƙara da cewa an ƙwace makamansu, ba tare da ba ƙarin bayani game da ainihin su ba.

Babu tsokaci nan-take daga sojin Isra’ila a kan rahoton.

Tun watan Okoban shekarar 2023, sojojin Isra’ila sun kashe fiye da mutum 70,000 a Gaza, yawancinsu mata da ƙananan yara, tare da jikkata fiye da mutum 170,900 a yaƙin na shekara biyu da ya lalata da yawa daga zirin.