Harin RSF na watan Oktoban 2025 a Al-Fasher na Sudan ya kashe aƙalla mutum 6,000: Rahoton MDD
Wani rahoto da ofishin kare haƙƙin bil’adama na MDD ya fitar, ya ce harin da dakarun RSF ɗin suka kai don karbe birnin Al Fasher ya ƙunshi mummunan abubuwa na zalunci wanɗanda suka haɗa da kisan kiyashi da fyade da sace mutane don neman kuɗin fansa.
Fiye da mutane 6,000 ne suka rasa rayukansu cikin fiye da kwanaki uku lokacin da rundunar sa-kai ta RSF ta ƙaddamar da "jerin hare-hare masu tsanani" a yankin Darfur na Sudan a karshen watan Oktoba, in ji Majalisar Dinkin Duniya.
Wani rahoto da ofishin kare haƙƙin bil’adama na MDD ya fitar, ya ce harin da dakarun RSF ɗin suka kai don karbe birnin Al Fasher ya ƙunshi mummunan abubuwa na zalunci wanɗanda suke daidai da laifukan yaƙi.
“Take-hakkokin da aka yi ba tare da tausayi ba da RSF da dakarun haɗin gwiwarsu suka aikata a harin ƙarshe kan el-Fasher sun nuna cewa rashin hukunci mai ɗorewa na ƙara janyo ci gaba da samun tashin hankali,” in ji Babban Kwamishinan MDD na hukumar kare haƙƙin ɗan’adam, Volker Türk.
RSF da dakarun haɗin gwiwarsu, wanda ake kira Janjaweed, sun mamaye Al Fasher, abin da ya rage wa sojojin Sudan a Darfur, a ranar 26 ga Oktoba kuma suka yi barna a cikin birnin da kewayensa bayan shafe fiye da watanni 18 suna yi masa ƙawanya.
Rahoton MDD mai shafi 29 ya bayyana jerin mummunan al'amura waɗanda suka haɗa da kisan kiyashi da fyade da sace mutane don neman kuɗin fansa da azabtarwa da rashin tausayi zuwa tsarewa da ɓacewar mutane. A lokuta da dama, harin ya kasance na kabilanci, in ji rahoton.