| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
RSF ta kai mummunan hari wani ƙauye a Darfur ta Arewa
Dakarun RSF sun kai hari ƙauyen Mastariha suka kuma ƙona gidaje da yawa, in ji wata kungiya mai zaman kanta ta Emergency Lawyers.
RSF ta kai mummunan hari wani ƙauye a Darfur ta Arewa
Ƙungiyar RSF ta kai mummunan hari wani ƙauye a Darfur ta Arewa / Reuters

Wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta Sudan a ranar Talata ta zargi dakarun ‘yan a-waren Rapid Support Forces (RSF), da kai wani mummunan hari ƙauyen Mastariha a Arewacin Darfur, a yammacin Sudan.

Kungiyar Emergency Lawyers (Lauyoyi na Gaggawa), wata ƙungiya mai zaman kanta, ta ce a cikin wata sanarwa cewa mayaƙan RSF sun kai farmaki Mastariha a ranar Litinin sannan suka ƙona gidaje da dama a ƙauyen.

Sanarwar ta ƙara da cewa kafin farmakin an fara da harin jiragen sama marasa matuki a wurare da dama, ciki har da cibiyar lafiya, kasuwa, wuraren masaukin baƙi da gidajen mutane, wanda hakan ya jawo raunuka da mutuwar wasu tare da tilasta wa da dama tserewa.

Ƙungiyar ta kira harin a matsayin "keta dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa da take haƙƙin ɗan’adam a fili."

Kira don bincike

“Wannan hari ya ƙara shiga tarihin keta dokoki a Darfur, wanda zai iya zama kisan kare dangi da laifukan da suka kai matsayin laifukan ƙasa da ɗan’adam, kuma yana nuna tsarin kai hare-hare ga fararen hula da dukiyoyinsu,” in ji ƙungiyar, tana kiran Kotun Duniya ta Hukunta Manyan Laifuka (ICC) da ta gudanar da bincike kan laifukan da aka aikata a Darfur, kuma ta gurfanar da waɗanda ke da alhaki kai-tsaye don tabbatar da kariyar fararen-hula.

Wasu 'yan RSF da dama sun kuma saka bidiyo daga Mastariha, in ji Hukumar Labarai ta Anadolu.

Sojoji suna riƙe da iko a mafi yawan jihohin Sudan, ciki har da babban birni Khartoum, yayin da RSF ke riƙe da jihohi biyar na Darfur ta yamma, sai dai wasu sassan Arewacin Darfur da suka kasance ƙarƙashin ikon rundunar soja.

Rikicin Sudan, wanda aka fara a watan Afrilun 2023, ya kashe dubban mutane kuma ya tilasta wa kusan mutane miliyan 13 yin gudun hijira, inda ya haifar da ɗaya daga cikin mafi munin rikicin jinƙai a duniya da yanayin yunwa, a cewar rahotannin Majalisar Dinkin Duniya.

Rumbun Labarai
Fafaroma Leo ya nufi Kamaru ƙasa ta biyu a ziyararsa ta Afirka
Yaƙi ya jefa fiye da kashi 70 cikin 100 na 'yan ƙasar Sudan cikin talauci, in ji MƊD
Yadda yakin Iran ke shafar tattalin arziki, yanki da siyasar Afirka
Za a cim ma yarjejeniyar bututun gas na Nijeriya-Maroko kan biliyan $25 a bana: Jami'i
Fafaroma Leo ya fara ziyararsa ta farko zuwa Afirka
Matsalar yunwa a Sudan: Miliyoyin mutane na cin abinci sau ɗaya a rana
Ana gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Jamhuriyar Benin
Shugaban ƙasar Djibouti Guelleh ya sake yin nasara karo na shida
Ana gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Djibouti inda Guelleh da ke mulki ke neman wa'adi na shida
Daga hanyoyin mulkin mallaka zuwa na korar mutane: Afirka da siyasar korar baƙi daga wata ƙasa
Yadda ajujuwan Afirka ke fuskantar jarrabawa mafi tsauri a duniya
Kamaru ta ce ‘yan kasarta 16 sun mutu yayin taya Rasha yaki da Ukraine
Dalilin da ya sa Kenya da Ethiopia suka zama manyan masana'antun furanni a duniya
Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 15 a Angola
Senegal ta haramta wa jami'an gwamnati tafiye-tafiye marasa muhimmanci zuwa ƙasashen waje
Yadda aikin dala miliyan 240 ke bai wa al’umar gaɓar teku a Benin da Mauritania damar gwagwarmaya
Gwamnatin Madagascar ta daƙile yunƙurin kashe shugaban ƙasar Michael Randrianirina
Sudan ta yi Allah wadai da 'mummunan' harin da RSF ta kai wani asibiti yayin allurar rigakafin yara
Ghana za ta fara aiwatar da shirin shiga ƙasar ba tare da biza ba ga dukkan 'yan Afirka
Shugaban riƙon jihar Kudu maso yammacin Somaliya zai hau kan mulki bayan ajiye aikin shugaba