| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Wakilan DR Congo da na M23 za su fara tattaunawar sulhu kai-tsaye a ranar 18 ga Maris — Angola
Angola ta ce za a fara tattaunawar a birnin Luanda bayan duka ɓangarorin biyu sun amince su hau kan teburin sulhu.
00:00
Wakilan DR Congo da na M23 za su fara tattaunawar sulhu kai-tsaye a ranar 18 ga Maris — Angola
A baya Tshisekedi ya ƙi amincewa da tattaunawa da ‘yan tawayen M23, waɗanda suka rinƙa kai hare-hare a gabashin DRC tare da goyon bayan Rwanda. / Reuters
13 Maris 2025

A ranar 18 ga watan Maris ne za a fara tattaunawa tsakanin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo (DRC) da 'yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda waɗanda suka kwace wasu yankunan gabashin DRC masu arzikin ma'adinai, kamar yadda Angolar ta bayyana.

Angola, wadda ita ce mai masaukin bai, ta ce za a fara tattaunawar a Luanda babban birnin ƙasarta

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar Angola ta fitar a ranar Larabar, ta ce, "Bayan matakan da kasar Angola ta dauka na shiga tsakani... tawagogin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da na M23 za su fara tattaunawar zaman lafiya kai tsaye a ranar 18 ga watan Maris a birnin Luanda."

Jerin tattaunawar zaman lafiya da Angola ta jagoranta a baya ba su yi nasarar dakatar da rikicin tsakanin sojojin Kongo da M23 ba.

Sai dai a ranar Talata, Angola ta bayyana cewa duka ɓangarorin biyu sun amince su haɗu a bisa teburin sulhu, bayan Shugaban DR Kongo Felix Tshisekedi ya tattauna batun rikicin tsakaninsa da takwaransa na Angola Joao Lourenco.

Sai dai duk da Luanda ta sanar da ranar tattaunawar, ba ta bayar da wani takamaiman lokacin da tattaunawar za ta fara.

A baya Tshisekedi ya ƙi amincewa da tattaunawa da ‘yan tawayen M23, waɗanda suka rinƙa kai hare-hare a gabashin DRC tare da goyon bayan Rwanda.

Sai dai Shugaban Angola Joao Lourenco a ranar Talata ya ce “tattaunawa kai tsaye” a tsakanin ɓangarorin biyu za ta faru nan da kwanaki masu zuwa, bayan ya tattauna da Tshisekedi.

A watan da ya gabata ƙungiyar ta M23 ta fito ta ce tana son amfani da hanyar maslaha domin kawo ƙarshen wannan rikicin.

Iko da ƙungiyar M23

Tun daga Janairu, M23 ta ƙwace muhimman biranen Goma da Bukavu kuma tuni ta fara mulki a yankunan da ke ƙarƙashin ikonta.

Tafiyar da ƙungiyar ke yi tana ƙwace birane ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 7,000 tun daga farkon 2025, kamar yadda DRC ta bayyana.

Sai dai Rwanda ta musanta ba M23 goyon bayan soji.

Sai dai wani rahoto na ƙwararru daga Majalisar Dinkin Duniya ya gano cewa Rwanda na da dakaru 4,000 a gabashin DRC domin goyon bayan ƙungiyar ta masu ɗauke da makamai.

Haka kuma Rwanda na da iko da ƙungiyar ta M23 domin ci gaba da tatsar arzƙin da DRC ɗin ke da shi a gabashin ƙasar waɗanda suka haɗa da zinari da kwalta, kamar yadda rahoton ya bayyana.

Domin tabbatar da goyon bayan da take yi wa M23, Rwanda ta yi nuni da kasancewar ƙungiyar masu ɗauke da makamai ta FDLR, wadda kungiya ce shugabannin ‘yan Hutu suka samar waɗanda ke da hannu a kisan kiyashin da aka aikata kan ‘yan ƙabilar Tutsi a Rwanda a 1994.