Israila ta rushe gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da sabon hari a Khan Younis
Sojojin mamaya na Isra’ila na ci gaba da rushe gidaje a unguwar Zeitoun, yayin da motocin soji ke luguden wuta sosai a gabashin birnin, kuma nau'uka daban-daban na jiragen sama marasa matuƙa na shawagi a yankin yammacin birnin.
Sojojin Isra’ila na ci gaba da rushe gidajen Falasɗinawa a unguwar Zeitoun da ke kudu maso gabashin birnin Gaza, yayin da suke kuma kai hare-hare ta sama masu ƙarfi kan birnin Khan Younis a kudu.
Sojojin mamaya na Isra’ila na ci gaba da rushe gidaje a unguwar Zeitoun, yayin da motocin soji ke luguden wuta sosai a gabashin birnin, kuma nau'uka daban-daban na jiragen sama marasa matuƙa na shawagi a yankin yammacin birnin.
Jiragen yaƙi na Isra’ila na kuma kai hare-haren sama masu tsanani a yankunan arewa da gabashin Khan Younis, yayin da aka harba makaman atilari na Isra’ila suka harba wasu bamabamai a yankin Zanna, da ke arewa maso gabashin birnin.
Yawancin rushe-rushen ana aiwatar da su ne a gaban wurin da aka shata “layin rawaya,” a cikin yankin da sojojin Isra’ila suka mamaye.
“Layin rawaya” na nufin yankin da sojojin Isra’ila suka janye zuwa gare shi bisa yarjejeniyar tsagaita wuta da ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba. Layi ne wanda ido bai iya gani wanda ya ratsa Gaza sannan ya raba yankin na Falasɗinawa gida biyu.
Adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru zuwa 241, yayin da wasu 619 suka jikkata, kuma an ciro gawawwaki 528.
Wannan ya sa jimillar adadin mutanen da suka mutu tun lokacin da Isra’ila ta fara yaƙin kisan kare dangi a Gaza a 7 ga Oktoban 2023 ya kai 69,176 sai kuma mutum 170,690 suka jikkata.