Dakarun Nijar sun cafke muggan makamai da aka yi safararsu daga Libya, sun kama masu safarar ƙwayoyi

Dakarun Garde Nationale na Nijar ne suka gudanar da waɗannan ayyuka a yankin Agadez bayan samun sahihan bayanan sirri game da wata mota da ke tafe daga Libya wadda ake zargi tana ɗauke da muggan makamai.

By
Waɗannan nasarori na nuna himmar dakarun Nijar wajen tabbatar da tsaron ƙasar daga barazanar kan iyaka.

Rundunar tsaro ta Garde Nationale ta Nijar ta samu nasara har sau biyu a yankin Agadez na ƙasar. Dakarun rundunar sun gudanar da manyan ayyuka guda biyu: na farko, cafke wata mota daga Libya ɗauke da makamai da harsasai masu yawa, sannan kuma sai kama wasu masu safarar miyagun ƙwayoyi dauke da sunƙin tabar wiwi mai yawa.

Waɗannan nasarori na nuna himmar dakarun Nijar wajen tabbatar da tsaron ƙasar daga barazanar kan iyaka.

A ranar 5 ga Nuwamba, bayan samun sahihan bayanan sirri game da wata mota da ke tafe daga Libya wadda ake zargi, an tura dakaru na musamman na Garde Nationale domin sa ido da aikin kame kilomita 65 arewa maso gabashin Agadez.

Bayan sun bi motar da ake zargi na tsawon lokaci, an tsayar da ita. A cikin motar, an cafke wasu masu safarar makamai uku ɗauke da muggan makamai masu yawa.

Makaman sun haɗa da bindigar Machine Gun da AK-47 biyu da fiye da harsasar 9,400 iri daban-daban da wayoyi tara  da katan uku na sigari da kuɗaɗen ƙasashen waje iri daban-daban da aka ɓoye a cikin kayayyakin masu safarar.

A cewar hukumomin yankin, wannan kamen ya nuna rawar da Agadez ke takawa a hanyoyin kasuwancin Sahara da kuma yadda dakarun Nijar suka ƙara kaimi wajen yaki da safarar abubuwa ta kan iyaka.

A mako guda kafin wannan, a ranar 27 ga Oktoba, 2025, wani aiki da dakarun na Garde Nationale suka yi ya kai ga kama masu safarar miyagun ƙwayoyi guda biyu dauke da ƙwallayen tabar wiwi 63 da kuma babura guda biyu da suke amfani da su wajen wannan haramtacciyar sana’a.

Waɗannan kamen da aka yi a jere suna tabbatar da yadda ayyukan Garde Nationale ke ƙaruwa a yankin, inda laifukan da ake aikatawa na kan iyaka – ciki har da safarar makamai, miyagun ƙwayoyi da mutane – suka zama babban ƙalubale ga tsaro.

Rundunar, wadda ke kan gaba wajen yaƙi da laifuka a yankunan hamada, ta tabbatar ta hanyar waɗannan ayyuka cewa tana da ƙudurin dakile duk wata barazana ga tsaron ƙasa.