Bikin al'adu na ƙamshin furen Vanilla na Malagasy da Ranar Uwa a Turkiyya
Ƙungiyar Al'adu da Haɗin kai ta Madagascar ta shirya wani taro na musamman na Ranar Uwa a Kocaeli, Turkiyya / AA
Bikin al'adu na ƙamshin furen Vanilla na Malagasy da Ranar Uwa a Turkiyya
Ƙungiyar Al'adu da Haɗin kai ta Madagascar ta yi bikin Ranar Uwa da wani taron al'adu na musamman wanda ya nuna ƙayataccen al'ada da fikirar yadda ake samar da ƙashim furen vanilla na Madagascar a duniya.

Bikin Ranar Uwa na Ƙungiyar Al'adu da Haɗin kai ta Madagascar mai cike da tarihi ya nuna ayyukan hanu musamman yadda ake sarrafa kamshin fure na vanilla na Malagasy wanda ya yi fice a duniya tare da haɓaka abota tsakanin al'adu a Turkiyya.

A bana ƙungiyar Al'adu da Haɗin kai ta Madagascar ta yi bikin Ranar Uwa inda ta gudanar da wani ƙataccen taro na musamman wanda ya haɗa al'adu, cimaka da haɗin kai a Kocaeli na ƙasar Turkiyya.

Bikin ya haskaka tarihin ƙamshin furen vanilla na Madagascar wanda ya shahara a duniya, haka kuma ya samar da wani dandanli na musayar al'adu da haɗin kai tsakanin mahalarta da suka fito daga wurare daban-daban.

A jawabinta a wurin taron, Shugabar Ƙungiyar Aymerillette Şen ta bayyana vanilla a matsayin fure da wuce iya dandano ko ƙamshi kawai, tana mai jaddada alaƙar da ke tsakanin furen da haƙuri da sadaukarwa da kuma al'ada da aka yi gadonsa.

"Vanilla wani nauyin abu ne na musamman daga fure zuwa ƙamshi," in ji ta. "Da ƙamshinsa mai daɗi, da darajarsa da kuma aikin hannu da ake yi wajen samar da shi, yana tunatar da mu game da rayuwar uwa."

Daga fure zuwa ƙamshi

Ƙamshin Valagasy vanilla yana dauke da tarihin al'adu mai yawa da kuma tattalin arzikin duniya, wanda ya kai kusan kashi 80 cikin 100 na yawan vanillar da ake samarwa a duniya.

An samo shi daga nau'in fure na orchid, vanilla ya kasance na biyu mafi tsada a duniya baya ga saffron.

Baya ga ƙamshinsa mai daɗi akwai wani tsari mai matuƙar wahala da ake bi wajen sarrafa shi. A Madagascar, inda ba a cika samun kwari masu raya rufen ba, dole manoma su yi amfani da hannayensu wajen raya ko wanne fure.

Ana buƙatar kusan furanni 600 don samar da kilogram ɗaya na vanilla, kuma kusan manoma 70,000 a faɗin ƙasar suna dogaro ne kan noman vanilla don gudanar da rayuwar yau da kullum.

Kazalika wadanda suka halarci taron sun koyi yadda ake amfani da Vanilla a tsarin warkarwa na gargajiya, ciki har da yin sirace da busarwa a rana da kuma tacewa - wani tsari da ke ɗaukar watanni masu yawa ana yi wanda daga ƙarshe yake samar wa vanilla ƙamshi, dandano da inganci na musamman.

Ƙayataccen ƙamshi

Bayan gabatarwar, baƙin sun samu damar ganin yadda ake samar da ƙayataccen kamshi mai daɗi ta hanyar turaren ruwa da kayan zaki da aka yi amfani da vanilla wajen sarrafa su, tare da samun damar halartar bitar yadda ake hada man lebe na vanilla wanda ya nuna yanda ake amfani da ainihin vanilla na Malagasy wajen samar da kayayyakin yau da kullun.

Şen ta ce manufar ƙungiyar ta wuce iya haɓaka al'adun Malagasy kawai, tana jaddada alƙawarinta na ƙarfafa alaƙa tsakanin baƙi da ke zaune a Turkiyya da kuma al'ummar ƙasar ta hanyar ayyukan al'adu waɗanda ke haɓaka tattaunawa, fahimta da haɗin kai a zamantakewa.

Ƙungiyar Al'adu da Haɗin kai ta Madagascar tana shirin ci gaba da shirya tarurruka na shekara-shekara waɗanda za su mayar da hankali kan muhimman abubuwan daban-daban na al'adu don ƙarfafa haɗin kai tsakanin al'adu da haɗin kai a zamantakewa.

Rumbun Labarai
Sirrin lafiyata: Shugaban Uganda Museveni ya ce ya kai kusan shekara 50 bai ci shinkafa ba
Nijeriya: An haramta wa 'yan ƙabilar Igbo naɗin sarautar gargajiya a ƙasashen waje
Nijeriya ta ƙwato kuraye biyu, beguwa da wasu tsuntsaye da ake ba wa kariya a wajen masu fasa-ƙwauri
Yadda Christina Koch ta daga tutar Ghana a yayin tafiyarta zuwa Duniyar Wata
Daga ƙasusuwa zuwa abin kwaɗayi: Orenge, abincin da ke sanya santi a Nairobi
Yadda A-Daidaita-Sahu na mata zalla ke sauya sufuri a jihar Kano ta Nijeriya
Kafafen sada zumunta na da alaƙa da raguwar farin ciki a faɗin Afirka da wasu yankuna - Rahoton 2026
Kuomboka: Ƙayatattun al'adun Masarautar Zambia mai shekara 300
Ƙalubalen sauyin yanayi a Afirka: Asarar rayuka, tafiyar ruwa da gidaje da rashin tabbas
An haifi wasu ‘yanbiyun gwaggwon biri da ke da wuyar samu karo na biyu a Congo DRC
Yadda raguwar kudin tallafi ke kai mutane kabari a Afirka
Yaya kaifin basira da fahimtar tausayi yake tsakanin giwaye?
Lailatul Qadri: Dare guda mai darajar watanni 1,000
Cutar kuturta a Afirka: Yanzu ne lokacin sauya lamarin
Mohbad: Taƙaddama game da ko marigayi mawaƙin Nijeriya shi ne uban ɗansa na asali
Mata da 'yanmata na cikin mafi munin bala'i da ƙasƙanci a Gaza - MDD
Azumi da Ciwon Suga: Shawarwarin ƙwararrun Lafiya ga Musulmai a watan Ramadan
An gano ƙwarangwal ɗin wata babbar dabbar dinosaur mai kama da tsuntsu a Hamadar Nijar
Yadda Harsuna 2,000 suka sa Afirka ta zama nahiya mafi yalwar lugga a duniya
Ramadan a Gaza: Falasɗinawa na kokawa kan yadda yaƙi ya hana su abubuwan da suka saba lokacin azumi