Kimanin mutum 1,430 ne aka raba da gidajensu a ƙauyuka biyar a jihar North Darfur ta Sudan a cikin yini ɗaya sakamakon ƙara munin rashin tsaro, kamar yadda hukumar kula da masu ƙaura ta Majasalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) ta bayyana.
Hukumar ukumar kula da masu ƙaura ta MƊD (IOM) ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis cewa kimanin mutum 1,430 sun tsere daga ƙauyukan Shatmarta da Sangari da Goz Laban da Dal Barida da Khair Wajid a yankin Umbro ranar Talata saboda ƙara tsanantan rashin tsaro.
Hukumar ta ce wasu daga cikin waɗanda aka raba da muhallansu sun ƙaura zuwa wasu wurare a cikin yankin Umbro, yayin da wasu suka tsallake kan iyaka zuwa ƙasar Chadi mai maƙwabtaka.
Ta ƙara da cewa yanayin tsaro a yankin “ya kasance na zaman ɗar-ɗar” da kuma cewa ta ci gaba da sa ido a kan yadda lamarin ke sauyawa.
Raba mutane da muhallansu na baya bayan nan na zuwa ne kwanaki uku bayan hukumar IOM ta ba da rahoton cewa kimanin mutum 2,260 sun tsere daga ƙauyuka biyu a Umbro sakamakon rashin tsaro.
Fararen hula masu tserewa
Ƙungiyar lauyoyi masu zaman aikin gaggawa wadda take zaman kanta ta ce dakarun RSF sun shafe kimanin wata ɗaya suna kai hare-hare kan ƙauyuka a Umbro, inda harin ya haɗa da kai samame kan kasuwanni da ƙona ƙauyuka da kuma ƙwashe kayayyakin mutane.
Dakarun RSF suna iko da huɗu daga cikin jihohin Darfur da kuma da yawa daga cikin jiha ta biyar ɗin , yayin da sojojin Sudan suka ci gaba da riƙe wasu ɓangarori na jihar North Darfur tare da yawancin jihohi 18 na ƙasar, ciki har da babban birnin ƙasar, Khartoum.
Darfur ya kai kashi ɗaya daga cikin biyar na girman ƙasar Sudan, wadda ta kai fiye da murabba’in kilomita miliyan 1.8 (murabba’in mil 695,000), yayin da yawancin mutanen ƙasar da aka ƙiyasta cewa adadinsu ya kai miliyan 50 suke rayuwa a wuraren da sojin ƙasar ke da iko.
Rikici ya mamaye Sudan tun wata Afrilun shekarar 2023, a lokacin da yaƙi ya ɓarke tsakanin sojin ƙasar da rundunar RSF game da shirye-shirye shigar da RSF ɗin cikin sojin ƙasar.
Yaƙin ya haddasa ɗaya daga cikin bala’in jinƙai mafi muni a duniya, inda ya kashe gomman dubban mutane tare da raba kusan miliyan 13 da gidajensu.












