Akalla sojojin Isra'ila takwas ne suka ji rauni a fafatawar da suka yi da mayakan Hezbollah a arewacin kogin Litani da ke kudancin Lebanon duk da yarjejeniyar tsagaita wuta na ɗan lokaci, a cewar kafofin watsa labarai na Isra'ila.
Gidan rediyon sojoji da Channel 14 a ranar Talata sun bayyana cewa sojojin sun ji rauni a wasu fafatawa uku kai tsaye da Hezbollah.
Rikicin ya barke ne bayan da sojoji daga rundunar Golani da rundunar Egoz suka ketare kogin Litani zuwa wajen Zawtar al-Sharqiyah, wani ƙauye mai nisan kilomita 10 daga kan iyakar Isra'ila, a cikin abin da rediyon sojoji ta bayyana a matsayin "farmakan" "kawar da makaman roka."
An ɗauki tsawon mako guda ana kai "farmakan" kuma an raunata sojoji da dama, in ji Rediyon Sojojin.
Channel 14 ta ce sojojin Isra'ila takwas sun ji rauni a fafatawar da suka yi da mayakan Hezbollah a yankin.
Kafofin watsa labaran ba su fayyace lokacin da sojojin suka ji rauni ko kuma lokacin da aka kai wadannan farmakai ba, suna cewa an ɓoye bayanan tare da hana su buga su har zuwa ranar Talata.
Babu wani bayani nan take daga Hezbullah game da rahoton.
Tun daga ranar 2 ga Maris, hare-haren Isra'ila a Lebanon sun kashe sama da mutane 2,869, sun kuma raunata sama da mutane 8,730, sannan sun raba sama da miliyan 1.6 da gidajensu, kimanin kashi ɗaya bisa biyar na al'ummar ƙasar, a cewar bayanan mahukuntan Lebanon.
Duk da tsagaita wutar da aka sanar a ranar 17 ga Afrilu kuma aka tsawaita har zuwa ranar 17 ga Mayu, sojojin Isra'ila suna ci gaba da kai hare-hare kowace rana a Lebanon, suna faɗaɗa mamayarsu da kuma rusa gidaje a ƙauyuka da dama a kudancin Lebanon.
















