Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci jami’an da za su jagoranci yaƙin neman zaɓensa su bayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu tare da haska fata duk lungu da saƙon ƙasar.
Kiran na shugaban ƙasar na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai bai wa Shugaba Tinubu shawara kan watsa labarai da dabaru kuma darakatan da ke jagorantar sadarwa na dabaru da watsa labarai na yaƙin neman zaɓen APC, Bayo Onanuga ya fitar ne ranar Asabar.
“Mun cika alƙawurranmu na yaƙin neman zaɓe kuma mun saka ƙasarmu a kan hanyar ci-gaban tattalin azriki,” kamar yadda sanarwar ta ambaci shugaban ƙasar yana cewa.
“Tabbas mun fice daga rami mai duhu kuma muna daf da cin gajiyar tattalin arziki mai wadata da zai fa’idantar da duk ‘yan Nijeriya,” in ji shi.
“Yadda muke shiga cikin kakar yaƙin neman zaɓe, muna da nasarori da yawa da za mu yayata—bari mu baje kolin tarihin aikinmu da kuma haska fata a duk lungu da saƙon ƙasarmu. Bari mu ci gagamarumar galaba a kan dukkan waɗanda ke neman mayar da ƙasarmu baya.”
Waɗanda aka naɗa a Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen
Sanarwar ta ce tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari shi ne zai kasance babban daraktan majalisar yaƙin neman zaɓen yayin da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma zai kasance sakataren majalisar.
Kazalika sanarwar ta ce Shugaba Bola Tinubu da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima za su kasance shugaban majalisar da mataimakin shugaban majalisar yaƙin neman zaɓen.
“Sanata Ajibola Bashiru da Hadiza Bala-Usman za su yi aiki a matsayin mataimakan sakataren,” in ji sanarwar.
Kazalika sanarwar ta ce shugaban majalisar, Shugaba Tinubu, zai yi aiki da masu ba da shawara da suka haɗa da Cif Bisi Akande da Cif Segun Osoba da Sanata Rochas Okorocha, da Sanata Abdullahi Adamu da Sanata Florence Ita Giwa.
“An naɗa shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, da Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abass, da Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe a matsayin mataimakan babban daraktan majalisar a kudu da arewa,” in ji Onanuga.
“Za su yi aiki da Sanata Bamidele Opeyemi da Sanata Jibril Barau a yankunan biyu,” in ji shi.
Kazalika sanarwar ta ce Sanata Adams Oshiomhole zai yi aiki a matsayin mataimakin babban darakta a fannin tattara jama’a yayin da shugaban ma’aikatan shugaban ƙasar zai yi aiki a matsayin mataimakin babban darakta da zai kula da gudanarwa.
James Abiodun Faleke, wanda ya taka rawa a yaƙin neman zaɓen 2023 zai yi aiki a matsayin mataimakin babban darakta na tsara zaɓe da sa ido da jagirantar yaƙin neman zaɓe, in ji sanarwar.
“ Faleke zai zaɓe daraktoci na yankuna da Sanata Olushola Adeyeye a Kudu maso Yammaci da Dakta Ngozi Olejeme a Kudu maso Kudu da Sanata Uche Ekwunife a Kudu maso Gabashi da Muntaqha Rabe a Arewa maso Yammaci da Ahmed Muhammed Ketso a Arewa maso Tsakiya da Sanato Sani Danladi a Arewa Maso Gabashi,” in ji sanarwar.
Kazaliak sanarwa ta ce Ms Stella Okotete da Injiniya Abdullahi Garba Ramat da Audu Maikori za su yi aiki a matsayin saktarori na ɓangaren tsara zaɓe.
Muiz Adeyemi Banire zai jagoranci fannin shari’a na majlisar inda Dakta Dr Liman Hassan da Babatunde Ogala za su aiki a matsayin masu taimaka masa. Sauran mambobin fannin sun haɗa da Prince Lateef Fagbemi da tsohon gwmana Ibrahim Shema da Worgu Boms da Dakta Kingsley Tochukwu Udeh, in ji sanarwar.
Bugu da ƙari ministar watsa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris Malagi, zai yi aiki a amatsayin darakta mai jagorantar dabarun sadarwa da kafafan watsa labarai tare da Dele Alake da Bayo Onanuga da Lanre Issa-Onilu, in ji sanarwar.
“Bangaren watsa labaran ya kuma ƙunshi Tunde Rahman da Sunday Dare da Daniel Bwala da kuma Felix Morka, waɗanda aka naɗa a matsayin mataimakan daraktoci masu jagoranci,” in ji sanarwar.
Abdulaziz AbdulAziz zai yi aiki da saura mutum uku Temitope Ajayi da Arabinrin Aderonke da kuma Frederick Nwabufor, a matsayin sakatarori masu jagoranci a ɓangaren watsa labarai na majalisar, in ji shi.
“Segun Dada zai yi aiki matsayin daraktan Kafafan Watsa Labarai Na Zamani, irin rawar da ya taka a shekarar 2022. Yayin da Solomon Arowolo zai yi aiki a matsayin sakatare, na Kafafan Watsa Labarai Na Zamani.
Kazalika majalisar yaƙin neman zaɓen ta naɗa mutum biyar a matsayin masu magana da yawunta a ƙarƙashin jagorancin Dele Alake. Sauran masu magana da yawun majalisar sun haɗa da Alwan Hassan da Ayobami Oyalowo da Kemi Asekun-Shittu da Adamu Fanda.
Shugaban ya buƙaci waɗanda aka bai wa muƙamai a cikin majalisar su tuntuɓi ‘yan jam’iyar waɗanda ba a saka sunayensu a cikin jerin sunayen waɗanda aka naɗa ba su taya su aiki.





















