Rundunar Sojin Nijeriya ta amince a tura ƙarin sojoji 850 zuwa Filato saboda matsalar tsaro

Wannan matakin ya biyo bayan harin da ya faru a daren Lahadi, 29 ga Maris, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka buɗe wuta a wata hanya mai cunkoso a Jos, inda suka kashe aƙalla mutane 28, ciki har da ɗalibai da ma’aikatan Jami’ar Jos.

By
An ɗauko sojojin ne daga rundunonin da ke Abuja da Kaduna, in ji sanarwar sojin / Reuters

Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Nijeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya amince da tura ƙarin sojoji 850 zuwa jihar Filato da ke fama da rikici, domin shawo kan matsalar tsaro da ke ƙaruwa.

Wannan mataki ya biyo bayan furucin Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, wanda ya ce mazauna yankin da jami’an tsaro an yi musu ba zata a lokacin harin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a Jos, yana mai bayyana lamarin a matsayin wanda ba a zata ba bayan dogon lokaci na zaman lafiya.

Sai dai, wata sanarwa daga Jami’in Yaɗa Labarai na Operation ENDURING PEACE, Kyaftin Chinonso Polycarpoteh, ta bayyana cewa tura ƙarin sojojin cikin gaggawa zai ƙarfafa ayyukan da ake yi a yanzu.

 “An tura ƙarin sojoji ne domin tallafa wa waɗanda ke bakin aiki wajen rage tashin hankali da kuma dawo da doka da oda a yankunan da abin ya shafa a jihar,” in ji wani ɓangare na sanarwar.

Yayin da yake jawabi ga sojoji a hedkwatar Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation ENDURING PEACE a Jos, Babban Hafsan Sojin ya umurce su da su kasance ƙwararru, masu ladabi da kuma tsayawa tsayin daka wajen fuskantar miyagun da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron al’umma masu bin doka.

Ya kuma tabbatar wa da sojojin cewa an samar musu da isassun kayan aiki da tallafin yaƙi domin tabbatar da nasarar aikin da aka ba su.

“Sabbin sojojin da aka tura, fiye da 850, an ɗauko su ne daga rundunoni a Abuja da Kaduna. An ɗora musu alhakin kare rayuka da dukiyoyi, tare da tabbatar da tsaro da lafiyar mazauna jihar baki ɗaya,” in ji sanarwar.

Wannan matakin ya biyo bayan harin da ya faru a daren Lahadi, 29 ga Maris, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka buɗe wuta a wata hanya mai cunkoso a Jos, inda suka kashe aƙalla mutane 28, ciki har da ɗalibai da ma’aikatan Jami’ar Jos.