Dakarun Juyin-Juya-Hali na Iran (IRGC) sun ce sun kai hari kan wani sansanin sojan sama na Amurka a Kuwait a matsayin martani ga wani farmakin jiragen sama na Amurka da aka kai kusa da Filin Jirgin Sama na Bandar Abbas a kudancin Iran.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Iran Tasnim da ke da dangantaka da gwamnati, IRGC ta ce an kai harin na ramuwar gayya da karfe 04:50 na asuba a ranar Alhamis, 'yan awanni bayan abin da ta bayyana a matsayin harin Amurka a wani wuri kusa da filin jirgin saman a birnin da ke gaɓar teku.
"Wannan martani gargaɗi ne mai tsanani domin abokan gaba su sani cewa harin ba zai tafi a banza ba, kuma idan aka sake kawo mana hari, martaninmu zai fi wannan ƙarfi," in ji bayanin.
Ba a ji wani martani nan take daga sojojin Amurka ba.
Tun da farko a ranar, wani jami’in Amurka ya ce rundunar Amurka ta kakkaɓo jirage huɗu marasa matuƙa na Iran waɗanda suke barazana a kusa da Mashigar Hormuz sannan ta hari kan wata tasha sarrafa sarrafa jiragen ta Iran a Bandar Abbas wadda ake zargin tana shirin tura na biyar.
"Waɗannan matakai an auna su, kuma na kare kai ne kawai, sannan an yi su ne don wanzar da tsagaita wuta," in ji jami’in, wanda ya yi magana bisa sharaɗin ba za a bayyana sunansa ba.
'Gagarumar saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta'
Sabbin hare-haren sun biyo bayan tabbatarwar da Rundunar Sojin Amurka ta CENTCOM ta yi a farkon wannan makon game da wasu hare-hare da aka kai a kudancin Iran kan wuraren harba makamai masu linzami da jiragen ruwa na Iran, da ake zargin suna ƙoƙarin dasa nakiyoyi. Iran ta yi Allah wadai da waɗancan hare-hare a matsayin "gagarumar saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta."
Tun da farko, da yake magana kan halin da tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin da ake yi da Iran take, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce "ba ya gamsuwa da ita, amma za mu gamsu. Ko dai hakan, ko kuma mu kammala aikin."
Tashin hankali a yankin ya sake kunnu kai ne a ranar 28 ga Fabrairu, lokacin da Amurka da Isra'ila suka kai hare-haren da ba a yi tsammani ba a kan Iran, abin da ya sa Tehran ta mayar da martani da harin jiragen sama marasa matuki da makamai masu linzami a fadin yankin, tare da rufe Mashigar Hormuz.
Tsagaita wuta ta fara aiki a ranar 8 ga Afrilu ta hanyar shiga tsakanin da Pakistan ta yi, amma tattaunawar da aka yi a Islamabad ba ta haifar da yarjejeniya mai ɗorewa ba.
Daga bisani Trump ya tsawaita zaman tsagaitawar wutar, yayin da ya ci gaba da hana jigilar jiragen ruwa da ke shiga ko fita daga tashoshin Iran ta wannan mahimmin hanyar ruwa, kana lokaci-lokaci yana cewa an kusa cimma yarjejeniyar ta zaman lafiya.










