Fidan na Turkiyya ya yi jerin tattaunawa da takwarorinsa kan kokarin kawo karshen yakin Iran
Hakan Fidan ya tattauna kan yanayin rikicin da kuma kokarin tsagaita wuta a tattaunawar da ya yi da jami’an kasashen China, Siriya, Qatar, da Uzbekistan.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya tattauna kan yakin da ake yi a Iran da takwaransa na Iran, Abbas Araghchi, da kuma takwaransa na Pakistan, Ishaq Dar, a cewar majiyoyin diflomasiyyar Turkiyya.
Majiyoyin sun bayyana cewa Fidan da Araghchi sun tattauna kan “halin da ake ciki yanzu a yakin” ta wayar tarho.
A wata tattaunawar daban ta wayar tarho, Fidan da Dar sun tattauna kan kokarin kawo karshen rikicin da ya barke sakamakon harin hadin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran.
Tun da farko, Fidan ya kuma gudanar da wasu tattaunawa ta wayar tarho na daban da takwarorinsa na kasashen China, Siriya, Qatar, da Uzbekistan domin tattauna yadda yakin ke gudana a yankin da kuma kokarin kawo kasrhen shi, in ji majiyoyin diflomasiyya.
A cewar majiyoyin Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya, Fidan ya tattauna da Ministan Harkokin Wajen Siriya, Asaad Hassan al Shaibani, Firaiminista kuma Ministan Harkokin Wajen Qatar, Mohammed bin Abdulrahman Al Thani, da kuma Bakhtiyor Saidov, Ministan Harkokin Wajen Uzbekistan.
Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan “yanayin yakin a yankin” da kuma shirye-shiryen da ake yi na “tsagaita wuta” a yakin, wanda aka fara a ranar 28 ga Fabrairu lokacin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar da harin hadin gwiwa kan Iran.
Fidan ya kuma tattauna ta wayar tarho da takwaransa na kasar China, Wang Yi, inda suka tattauna kan halin da ake ciki a yankin, in ji majiyoyin diflomasiyyar Turkiyya.
Yayin tattaunawar ta wayar tarho, ministocin biyu sun jaddada cewa dole ne a kawo karshen yakin da ake yi a Gabas Ta Tsakiya cikin gaggawa, sannan suka tattauna kan kokarin da ake yi ta wannan fanni.
Ministocin biyu sun bayyana cewa tabbatar da dorewar zirga-zirga, samar da makamashi, da hanyoyin samar da kayayyaki (supply chains) na da matukar muhimmanci.
Bangarorin biyu sun kuma tattauna kan batutuwan da suka shafi kasashensu, musamman dangantakar tattalin arziki da ciniki, da kuma zuba jari tsakanin juna.
Kasar China ta yaba wa Turkiyya
Ministan Harkokin Wajen kasar China, Wang Yi, ya nuna goyon baya ga “rawar da Turkiyya ke takawa” wajen inganta tattaunawar samar da zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya ruwaito.
Wang ya ce Beijing tana goyon bayan Turkiyya wajen “taka muhimmiyar rawa wajen inganta komawa teburin tattaunawa.”
Haka kuma, Wang ya bayyana goyon bayansa ga kasashen yankin da su “kwantar da hankulansu” sannan su “mayar da martani cikin hikima ga halin da ake ciki yanzu, tare da duba moriyar kasashensu na dogon zango.”
“Gaskiya da karya a wannan rikici na Gabas Ta Tsakiya a fili suke, kuma ya kamata kasashen duniya su dauki matsaya ta adalci,” in ji Wang, yayin da yake nuna cewa rikicin yana bazuwa cikin sauri a fadin yankin.
Ya kara da cewa, babban abin da ya kamata a ba fifiko shi ne “shiga tsakani don tattaunawar zaman lafiya, yin amfani da damar samar da zaman lafiya, da kuma kokarin kwantar da tarzoma.”