Shugaban ƙasar Benin, Romuald Wadagni, ya yi garambawul ga manyan hafsoshin rundunar sojin ƙasar a ranar Laraba, bayan kusan shekara ɗaya da daƙile yunƙurin juyin mulki a ƙasar.
A watan Disambar 2025 ne sojojin Benin suka hana yunƙurin da wasu jami'an soja suka yi na hamɓarar da tsohon shugaban ƙasar, Patrice Talon, inda Nijeriya ta taimaka wajen daƙile shirin.
Wannan sauyin shugabancin sojin na zuwa ne a daidai lokacin da Benin ke fuskantar ƙarin barazanar hare-haren 'yanta'adda a yankunan arewacin ƙasar.
Wadagni, wanda ya hau kan mulki bayan lashe zaɓen watan Afrilu, ya naɗa Janar Abou Issa a matsayin sabon shugaban rundunar sojin ƙasar, wanda zai maye gurbin Janar Fructeux Gbaguidi.
Ana sa ran Gbaguidi zai zama babban sakatare na dindindin na Majalisar Tsaro da Tsaron Ƙasa.
Haka kuma, an naɗa Kanal Andre Dokoui Fofo a matsayin shugaban rundunar sojin ƙasa, yayin da Kanal Herve Setondji Allotchenou zai jagoranci rundunar sojin sama.
Shi kuma Kyaftin Dossa Hounkpatin zai jagoranci rundunar sojin ruwa.
Wadagni, wanda ya shafe shekaru 10 yana riƙe da muƙamin ministan tattalin arzikin ƙasar Benin, ya karɓi ragamar shugabancin ƙasar ne a lokacin da matsalar tsaro a arewacin ƙasar ke ƙamari.





















