Tinubu ya umarci manyan hafsoshin tsaron Nijeriya su koma Maiduguri da zama

Rundunar ‘yansanda da hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA sun tabbatar da cewa mutum ashirin da uku ne suka mutu sakamakon hare-haren na ƙunar-baƙin-wake.

By
Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu / User Upload

Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, ya umarci manyan hafsoshin tsaron ƙasar su tattara kayansu su nufi Maiduguri, babban birnin jihar Borno, da zama bayan hare-haren ƙunar-baƙin-wake a wurare uku a birnin ranar Litinin.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, mai magana da yawun shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya ce Tinubu ya yi jimamin kisan mutanen da kuma tausaya wa waɗanda suka jikkata tare da yin alhini ga mazauna jihar.

“Ina so na bayyana ƙarara cewa wannan aika-aikar ta’addancin ƙoƙarin gaggawa ne na yankan-ƙauna na ƙarshe da masu aikata laifuka da ‘yanta’adda ke yi domin sanya tsoro a zukatan jama’a, saboda sun ga suna shan matsi babu ƙaƙƙautawa daga dakarun tsaronmu da ke aiki a wurare daban-daban,” in ji sanarwar.

“Za mu ci gaba da zafafa hare-harenmu kan dukkan masu aikata laifuka, a duk inda suke.”

Rundunar ‘yansanda da hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA sun tabbatar da cewa mutum ashirin da uku ne suka mutu sanadin hare-haren.

A ranar Litinin rundunar Operation Hadin Kai da ke yaƙar ta’addanci a arewa maso gabashin Nijeriya ta ce zai yiwu a sake samun ƙarin ‘yan ƙunar-baƙin-wake a Maiduguri.

Jami’in watsa labaran rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba ya ce hakan ne ya sa suka tura jami’an ɓangaren kawar da bamabamai na ‘yansanda domin kamo sauran ‘yan ƙunar-baƙin-waken.

A sanarwar, shugaban ya ƙara da cewa Nijeriya ba za ta miƙa wuya ga masu sanya tsoro a zukatan jama’a ba.

“Dole na yaba wa ƙarfin hali da kuma jajircewar dakarunmu masu kishin ƙasa waɗanda suka yi nasarar daƙile hare-haren da ‘yanta’addan nan kan sansanonin soji a jihar,” in ji Tinubu.

“Hare-haren ranar Litinin aika-aikar yankan-ƙauna ce ta ƙungiyoyin ‘yantadda masu zuciyar shaiɗanu. Jaruman sojojinmu da ‘yan sa-kanmu za su murƙushe su su kuma ƙasƙantar da su.

“A makon da ya wuce, yayin tattaunawa ta tsaro da shugabannin rundunonin tsaro da na tattara bayanan sirri, na amince a bayar da ƙarin kayayyaki da tallafi domin inganta aikinsu. Wannan ƙoƙarin ya riga ya fara aiki,” a cewar shugaban Nijeriya.

Ya ce, “Bugu da ƙari, na ba da umarnin cewa manyan hafsoshin tsaro su koma Maiduguri domin jagorantar lamarin. Na kuma ba da umarnin cewa hukumomin ba da agajin gaggawa su ba da kulawa da ta dace ga waɗanda lamarin ya shafa.

“Babu wani wuri a Nijeriya da ‘yanta’adda za su samu tsaro. Za mu gano inda suke, za mu yi arangama da su kuma za mu ba su kashi.

“Nijeriya ba za ta miƙa wuya ga tsoro ba,” in ji shugaban ƙasar.