| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Ayarin motocin sojin Aljeriya ya isa birnin Arlit na Nijar
A makon da ya gabata ne Majalisar Ƙasa ta Aljeriya ta amince da tura wani ɓangare na sojojin ƙasar zuwa Nijar don tabbatar da tsaron ayyukan man fetur na kamfanin Sonatrach na Aljeriya da ke aiki a Nijar ɗin.
Ayarin motocin sojin Aljeriya ya isa birnin Arlit na Nijar
Aljeriya ta bayyana cewa manufar tura dakarun ita ce kare muradunta na makamashi da tattalin arziki a Nijar

Wani ayarin motocin sojojin ƙasar Aljeriya ya isa Nijar, wanda wannan shi ne karo na farko da ƙasar ta tura irin waɗannan dakaru wata ƙasa tun bayan aika dakarunta domin tallafa wa Masar a lokacin yaƙin Larabawa da Isra'ila na shekarar 1973.

A cewar wasu mutane 10 da suka zanta da kamfanin dillancin labarai na Reuters, ayarin sojojin ya isa birnin Arlit, wanda ya shahara wajen haƙar ma'adinin Uranium, a arewa maso yammacin Nijar.

Aljeriya ta bayyana cewa manufar tura dakarun ita ce kare muradunta na makamashi da tattalin arziki a Nijar, sai dai ba ta bayyana adadin sojojin da ta tura ba ko kuma lokacin da za su isa.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da Nijar ke ci gaba da yaƙi da ƙungiyoyin 'yanta'adda masu alaƙa da Al-Qaeda da Daesh a yankin Sahel na Afirka ta Yamma.

Aljeriya, wadda ke da iyaka da Nijar, ta daɗe tana ɗaukar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan Sahel da Sahara a matsayin muhimmin ɓangare na tsaron ƙasarta. Haka kuma, tana da manyan muradun tattalin arziki a Nijar, musamman a ɓangaren makamashi.

Kamfanin mai da iskar gas na ƙasar Aljeriya, Sonatrach, mallakin gwamnati, yana da jarin kasuwanci a Nijar.

Haka kuma, akwai wani babban aikin samar da bututun iskar gas na Trans-Saharan, wanda ya ƙunshi ƙasashen Aljeriya, Nijar da Nijeriya. Aikin na da manufar jigilar iskar gas daga Afirka zuwa Turai da sauran kasuwannin duniya.

Matakin tura dakarun ya kuma nuna alamun inganta dangantakar diflomasiyya tsakanin Algiers, babban birnin Aljeriya, da Yamai, babban birnin Nijar, bayan takun-saka da aka samu a tsakaninsu a bara.

Nijar na da dumbin arzikin ma'adinan Uranium, man fetur da zinare, lamarin da ya sanya ƙasar take da matuƙar muhimmanci ta fuskar tsaron yankin da kuma muradun tattalin arziki.