Sabon Alƙalin Alƙalan Ghana Baffoe-Bonnie ya fara aiki

Ranar Alhamis ne dai majalisar dokokin ƙasar ta amince da sunan alƙalin da shugaban ƙasar ya miƙa mata a matsayin sabon alƙalin alƙalan ƙasar.

By
Shugaba John Mahama ya rantsar da maishari'a Baffoe-Bonnie a matsayin alƙalin alƙalan Ghana

Maishari’a Paul Baffoe-Bonnie ya kama aiki a matsayin sabon Alƙalin Alƙalan ƙasar Ghana na tara tun bayan da ƙasar ta fara jamhuriya ta huɗu.

Shugaba John Dramani Mahama ne ya rantsar da shi a fadar gwamnatin ƙasar da ke Accra  ranar Lititin a wani bikin da alƙalan manyan kotuna suka halarta tare da ‘yan’uwan alƙalin da ‘yan majalisar dokoki da manyan jami’an gwamnati.

A ranar Alhamis ne majalisar dokokin ƙasar ta amince da sunan alƙalin da Shugaban Ƙasar ya miƙa mata a matsayin sabon Alƙalin Alƙalan ƙasar.

Kafin a rantsar da shi, alƙalin yana aiki ne a matsayin muƙaddashin Alƙalin Alƙalan ƙasar tun ranar 22 ga watan Afrilun shekarar, 2025.

Da yake rantsar da Maishari’a Baffoe-Bonnie, Shugaba Mahama ya ce dole ya kasance mai ɗabi’u na adalci da ‘yanci da gaskiya kamar yadda aka tsara a kundin tsarin mulkin shekarar 1992.

Ƙarfin Dimokraɗiyyar Ghana, a cewar Shugaban Ƙasar, ya dogara ne ga ga daidaiton iko tsakanin ɓangarorin gwamnati uku – ɓangaren zartarwa da ɓangaren dokoki da kuma ɓangaren shari’a – inda za su yi aiki da ‘yanci amma kuma da haɗin kai domin jin daɗin ‘yan Ghana.

“A matsayin shugaba, na yi sha alwashin jajircewa na ga tabbatar da ‘yancin ɓangaren shari’a,” kamar yadda Shugaba Mahama ya bayyana.

“Ɓangaren shari’a mai ‘yanci ba tallafi ba ne kawai ga kotuna. Buƙata ce wadda kundin tsarin mulki ya yarda da ita da kuma kare kowane ɗan ƙasa da ciki har da Shugaban Ƙasar,” in ji shi.

Ya yi kira ga Maishari’a Baffoe-Bonnie ya aiwatar da aikinsa ba tare da sani ko sabo ba.

Yayin da mutane ke rage yarda da hukumomin gwamnati, Shugaba Mahama ya ce dole ɓangaren shari’a ya kasance ya fi ƙarfin zargi domin wani jami’in shari’a ya aikata cin hanci ɗaya zai iya lalata shekaru na aiki tuƙuru da da kuma yardar da al’umma ke da shi kan ɓangaren gabaɗaya.