Turkiyya za ta samar da 'ƙwararan' shirye-shiryen makamashin lantarki da Ethiopia

Ministan makamashi ya ce burinsu shi ne ƙarfafa haɗin kai a fannin wutar lantarki da kayayyakin aikin wuta da saka jari a makamashin da ake sabuntawa da kuma tashoshin samar da wuta ta ruwa.

By
Shugaba Erdogan da Firayim Minista Abiy sun jagaoranci yarjejeniyoyi tsakanin Turkiyya da Ethiopia , da ta JEC ta 9 . / AA

Turkiyya na son ƙarfafa alaƙarta a fannin makamashi ga Ethiopia tare da samar da ƙwararan ayyuka da kuma zurfafa haɗin kan da ke tsakanin ƙasashen biyu a fannoni daban-daban, kamar yadda ministan makamashi da ma’adinan Turkiyya Alparslan Bayraktar ya bayyana ranar Talata.

Ma’aikatar makamashi da ma’adinan Turkiyya da ma’aikatar ruwa da makamashi ta Ethiopia sun rattaba hannu kan yarjejeniya ta haɗin kai a fannin makamashi wanda Bayraktar da ministan ruwa da makamashin Ethiopia Habtamu Itefa suka sanya wa hannu ranar Talata yayin ziyarar aikin Shugaba Recep Tayyip Erdogan zuwa Addis Ababa.

A ƙarkashin yarjejeniyar, ƙasashen biyu za su samar da ayyuka na haɗin gwiwa a fannonin lantarki da makamashin da za a iya sabuntawa da kuma inganta aiki da makamashi da kuma haɗin kai wajen samarwa da kuma haɗa kayayyakin tashar samar da makamashi ta ruwa da kuma farfelun samar da lantarki.

Zuba jari na gwamnati da na ‘yan kasuwa cikin ayyukan samar da makamashi da samar da lantarki da dakon lantarki da kuma rarraba lantarki za su samu tallafi, kuma za a tabbatar da musayar ƙwarewa tsakanin hukumomi masu ruwa-da-tsaki, in ji ministan.

"Muna da niyyar ƙarfafa musayar ƙwarewa da kuma samar da ayyuka a fannoni daban-daban daga samar da lantarki da kayayyakin aikin makamashi da zuba jari a makamashin da ake sabuntawa da kuma ayyukan samar da lantarki ta ruwa," kamar yadda Bayraktar ya wallafa a shafin sada zumunta na Turkiyya NSosyal.

"Mun cim ma yarjejeniya kan wani cikakken tsari na zurfafa haɗin kanmu da kuma aiwatar haɗin kai a sabbin ɓangarori daban-daban daga makamashi da haƙar ma’adinai da ilimi da lafiya da sufuri da noma da muhalli da tsara birni da al’adu da kuma yawon buɗe ido," in ji shi.