Trachoma: Ta'azzarar amosanin ido da ke makanta mutane na ƙarfafa fafutukar dawo da gani a Afirka
Yawan mutanen da ke cikin hatsarin kamuwa da cutar da ke jawo makanta ya ragu sosai zuwa ƙasa da miliyan 100 a karon farko a duniya, inda hanyoyin da ake bi don magance cutar a Afirka ke tasiri sosai.
Har yanzu tana jin sautin dariyar jikokinta, cikin nishaɗi kuma a kurkusa da ita, sai dai kash, a hankali ta daina ganin fuskokinsu.
A duk lokacin da ta so taimakawa da ayyukan gida, sai rashin ido ya sagar mata da gwiwa.
Cutar trachoma ta raba Abeba Mengesha da duk wani jin daɗin rayuwa. Tsananin ciwo na cutar ya ƙarar mata da duka gashin idonta tare da makantata dunɗim.
“A hankali na daina ganin komai sai duhu,” in ji tsohuwar mai shekara 68 ‘yar wani ƙauye a ƙasar Habasha,” a hirarta da TRT Afrika. “Na dinga jin tsoron kar na zame wa mutane lalura.”
Wata ‘yar ƙaramar tiyata, wacce aka yi mata a ƙarƙashin fafutuka ta wata cibiyar lafiya a yankin, ta gyara matsalar da a baya Abeba ta yi zaton ta gama lalata rayuwarta ke nan.
“A ranar da suka cire bandejin, sai na ji giftawar haske. Ba wai haske ne kawai ya sake ratsa idona ba; rayuwata ce ta dawo gaba ɗaya.” in ji Abeba.
“A yanzu ina iya ganin jikokina. Ina iya ɗebo ruwa; ina iya yin sauran ayyuka. Gani shi ne komai a rayuwa.
Labarin Abeba, wanda ya taɓa zama mai taɓa zuciya abu ne da ya zama ruwan dare a ƙasashen Afirka, hujja ce da ke nuna yadda ake yin nasara a yaƙi da cutar ido ta trachoma.
Samun sauyi
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta sanar a watan Disamban 2025 cewa a karon farko a tarihi, yawan mutanen da ke neman a yi musu aikin ido na cutar trachoma - wacce ita ce ta fi jawo makanta - ya ragu sosai zuwa ƙasa da miliyan 100.
Daga mutum biliyan 1.5 da ke fuskantar barazanar makancewa sakamakon amosanin ido a shekarar 2002, a yanzu alƙaluman sun ragu da kashi 94 cikin 100 inda adadin ya koma miliyan 97.1.
A Kenya, ma'aikacin lafiyar al'umma Samuel Kariuki ya yi nazari kan jerin cututtukan da ke yaɗuwa wanda ya zama babban nauyi da ba za a iya shawo kansa ba ga shirye-shiryen kiwon lafiya da ke rage yaɗuwar cutar, musamman a nahiyar.
"Shekaru 20 da suka wuce, cutar trachoma ta yaɗu ko ina. Magunguna da tiyata kaɗai ba su kawo wani canji ba. Godiya ga kamfen ɗin yaƙi da cutar, mutane yanzu sun fahimci mahimmancin ingantacciyar tsafta. Muna ƙoƙarin kawar da cutar trachoma," in ji shi a hirarsa da TRT Afrika.
Amma Samuel ya yi magana cikin taka tsantsan. "Amma ba za mu iya daina yaƙi da cutar ba. Za mu iya hutawa, amma ƙwayoyin cuta (Chlamydia trachomatis) da ke haifar da kamuwa da cutar da ƙudaje da ke taimakawa wajen yaɗuwarta ba za su tsagaita ba. Raguwar kamuwa da cutar na ƙara mana ƙaimi har sai mun kawo ƙarshen cutar," in ji shi.
Ana samun raguwar kamuwa da cutar ne sakamakon shekaru da dama da aka shafe ana ƙoƙari mai ɗorewa na kawar da ita a ƙarƙashin dabarun SAFE da WHO ta amince da shi - da yin tiyata, da rigakafi da tsaftace fuska da kuma inganta muhalli.
Ganin cewa WHO ta tabbatar da Masar da Fiji a matsayin waɗanda suka kawar da cutar a matsayin matsalar lafiyar jama'a, jerin sun ƙaru zuwa ƙasashe 27, waɗanda suka mamaye kowane yanki da cutar trachoma ta fi kamari.
"Rage yawan masu cutar amosanin ido zuwa ƙasa da miliyan 100 shaida ce ta ƙarfin jagoranci a ƙasa da kuma aiwatar da dabarun SAFE akai-akai," in ji Dr Daniel Ngamije Madandi, darektan sashen cututtukan zazzabin cizon sauro da aka yi watsi da su a wurare masu zafi a WHO.
"Bayanan sun nuna cewa SAFE yana da tasiri kuma yana daidaitawa. WHO ta ci gaba da jajircewa wajen tallafa wa ƙasashe don cim ma nasarar kawar da cutar trachoma a duniya nan da shekarar 2030."
Ƙokarin ƙasashen duniya
Kamfanonin harhaɗa magunguna sun ba da gudunmawar magungunan yaƙi da cutar har biliyan 1.1 da suka hada da azithromycin, wanda ake amfani da shi don yaƙar cutar, duk a ƙarƙashin shirin Trachoma Initiative (ITI).
Shirye-shirye masu kama da juna kamar Global Trachoma Tapping Project da wanda ya gaje shi, Tropical Data, sun shafi mutane fiye da miliyan 15, wanda hakan ya bai wa ma'aikatun kiwon lafiya damar kai dauki cikin daidaito - inda ake duba mutum daya a duk bayan dakika 25 tun daga shekarar 2012.
"A bayan kowane ci gaba akwai miliyoyin labaran mutanen da aka kare idanunsu," in ji PJ Hooper, darektan ITI.
Babban ƙalubalen da ake fuskanta wajen cim ma burin kawar da cutar trachoma nan da shekarar 2030 shi ne kusan mutane miliyan 100 ne ke cikin haɗari, yawancinsu suna cikin yankunan da ba a ba su kulawa sosai.
"Raguwar kashi 94% tun daga shekarar 2002 abin mamaki ne," in ji Michaela Kelly, shugabar ƙungiyar ƙasa da ƙasa ta yaƙi da cutar Trachoma.
"Muna buƙatar kusan dala miliyan 300 don cike gibin kuɗi a fannin tiyata da samo maganin rigakafi da ƙarfafa bincike."
Abeba, wacce yanzu take rayuwar da a baya har ta fitar da rai da ita, ta bayyana godiyarta ga wannan ƙoƙari da ya dawo mata da ganinta.
"Ka gaya musu aikinsu ba wai kawai game da adadi ba ne," in ji ta. "Sun ba ni idanu da kuma makoma mai kyau."
Ma'aikacin lafiya Samuel yana jin cewa an kusa samun nasara. "Mun nuna cewa za a iya shawo kan wannan cuta. Yanzu, dole ne mu tabbatar da cewa gaɓa ta ƙarshe ba ita ce mafi wahala ba."