| Hausa
KIMIYYA DA FASAHA
2 minti karatu
NASA ta ƙaddamar da shirin Artemis II, ta tura 'yan-sama-jannati 4 Duniyar Wata bayan shekara 53
Shirin yana son mayar da bil'adama duniyar wata bayan gomman shekaru , inda 'yan sama jannati huɗu ke tafiya mai cike tarihi zuwa duniyar wata.
NASA ta ƙaddamar da shirin Artemis II, ta tura 'yan-sama-jannati 4 Duniyar Wata bayan shekara 53
NASA ta ƙaddamar da shirin Artemis II, ta tura 'yan-sama-jannati 4 Duniyar Wata bayan shekara 53 / Reuters
kwana ɗaya baya

Hukumar Sararin Samaniyar Amurka NASA ta tura ‘yan-sama-jannati hudu zuwa Duniyar Wata, a tafiyar bil’adama ta farko zuwa can cikin fiye da shekaru 50.

An harba Kumbon Artemis II daga cibiyar sararin samaniya ta tunawa da Kennedy da ke Florida, tare da ‘yan-sama-jannatin zuwa sararin samaniya.

Jirgin zuwa Duniyar Watan mai suna Orion a yanzu yana kan hanyarsa ta tafiyar kwanaki goma da zai zagata DUniyar Watan kafin ya dawo duniyarmu.

Jami’an sun haɗa da ‘yan-sama-jannatin Amurka guda uku da wani ɗan-sama-jannati na ƙasar Kanada, a wata tafiya da aka yi domin gwada muhimman tsare-tsaren da ake buƙata wajen binciken can cikin sararin samaniya a nan gaba.

‘Yan-sama-jannatin za su shiga kewayen Duniyar Wata, inda za su shafe kwanaki suna gwaje-gwaje kafin su fara yawo kusa da Wata, in ji bayanan bidiyon NASA na kai-tsaye.

Komawa duniyar wata

Tafiyar ce karon farko da jirgin shiga sararin samaniya ya ɗauki mutane zuwa asalin tauraron na duniya cikin fiye da shekara 50.

NASA ta ce ta tura jirgin na wakiltar wani muhimmin ci gaba a shirinta na Artemis, da ke ƙoƙarin mayar da bi’ladama Duniyar Wata daga baya a cikin shekaru goman nan da kuma tallafa wa bincike na can cikin sararin samaniya.

Ana kuma kallon tafiyar a matsayin muhimmin mataki wajen tabbatar da kasancewar bil’adama mai ɗorewa a Duniyar Wata, ciki har da da wani sansani na duniyar wata da abokan aiki na ƙasashen duniya.

Sai dai kuma ana kan gina muhimman tsare-tsare, musamman jirgin sauka kan Duniyar Wata ne, inda NASA take aiki domin hanzarta ci gaban aiki daga ‘yan kwagila kamfanonin SpaceX da Blue Origin.

Jami’ai sun yi shirin gwada ɗaya ko duka biyu daga cikin jiragen sauka a Duniyar Watan a kewayen duniya kafin su yi ƙoƙarin sauka a duniyar wata, inda aka shirya wata tafiya ta gwaji a shekara mai zuwa.