Babban birnin Mali Bamako na fuskantar ƙarancin man gas
Ƙasar Mali wadda ba ta da teku ta dogara ne kan shigowa da mai ta manyan motocin dakon mai kuma a baya bayan nan tana fama da ƙarancin mai sakamakon hare-haren ‘yanta’adda kan jerin gwanon motocin dakon mai.
Direbobi a babban birnin Mali suna fuskantar ƙarancin man gas saboda yanzu kamfanin makamashi na ƙasar ya fi amfani da man domin ƙasar ta kauce wa yawan ɗaukewar lantarki, in ji ƙungiyar kamfanonin man ƙasar ranar Talata.
Ƙasar Mali wadda ba ta da teku ta dogara ne kan shigowa da mai ta manyan motocin dakon mai kuma a baya bayan nan tana fama da ƙarancin mai sakamakon hare-haren ‘yanta’adda kan jerin gwanon motocin dakon mai.
Tun watan Satumba, ‘yanta’adda masu alaƙa da Al Qaeda suna ta yunƙurin gurgunta tattalin azikin Mali ta hanyar hana shigar da mai.
‘Yanta’addan sun kuma kai hari kan tankokin man da ke shiga Mali tare da toshe wasu muhimman hanyoyin shiga babban birnin ƙasar, Bamako.
Dogayen layuka
An samu ƙaruwar samar da mai tun watan Disamba, lamarin da ke sa tattalin arzikin ya farfaɗo.
Amma a baya bayan nan, man gas ya ƙare a wasu gidajen mai a Bamako.
Ranar Talata an samu layuka masu tsawo a gidajen man Bamako, kamar yadda wani ɗan jarida na kamfanin dillancin labaran AFP ya bayyana .
"Manyan motoci da ke dakon yashi da duwatsu sun daina aiki" saboda ba sa iya samun man gas, kamar yadda ƙungiyar masu samar da yashi ta shaida wa AFP.
Katse hanyoyin sufuri
Kafofin watsa labaran ƙasar sun ce fiye da motoci 100 da ke jigilar mutane sun daina aiki a Bamako ranar Litinin saboda rashin mai.
"Man gas dai an fi tanadarsa domin kamfanin makamashin Mali (EDM)" wanda ke shan matsi saboda tsananin zafi, kamar yadda wani mamba na ƙungiyar kamfanonin mai ya shaida wa AFP.
A Bamako da sauran yankuna da ke kewaye da shi, wannan ya yi tasiri kan samun wuta a kwanakin nan.
A ƙarshen watan Janairu, ƙungiyar ‘yanta’adda da ke aika-aika a Mali "ta yi wa direbobin manyan motoci 10 da matasa biyu masu koyon aiki kisan gilla" a kusa da kan iyakar ƙasar Senegal, in ji wata ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta ƙetare.