| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Hukumar INEC ta Nijeriya ta tsawaita aikin rajistar masu zaɓe da makwanni biyu
Hukumar INEC ta ce ta ɗauki wannan matakin ne bayan la’akari da ra’ayoyin da ta samu daga ofisoshinta na jihohi, jam’iyyun siyasa, ƙungiyoyin fararen-hula da sauran masu ruwa da tsaki.
Hukumar INEC ta Nijeriya ta tsawaita aikin rajistar masu zaɓe da makwanni biyu
An fara aikin rajistar ne a ranar 18 ga Agustan 2025, kuma tun da farko an tsara cewa za a kammala a ranar 10 ga Yulin 2026. / Reuters

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC) ta tsawaita aikin rajistar masu zaɓe da ake gudanarwa a faɗin ƙasar da makwanni biyu.

An fara aikin rajistar ne a ranar 18 ga Agustan 2025, kuma tun da farko an tsara cewa za a kammala a ranar 10 ga Yulin 2026.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ƙasa kuma Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Ilmantar da Masu Zaɓe, Mohammed Haruna ya fitar a ranar Jumma’a, ya ce hukumar ta yanke shawarar tsawaita aikin ne bayan la’akari da ra’ayoyin da ta samu daga ofisoshinta na jihohi, jam’iyyun siyasa, ƙungiyoyin fararen-hula da sauran masu ruwa da tsaki.

Kwamishinan ya bayyana cewa sabon tsarin yin rajista na yi-da-kanka (self-service) zai bai wa ’yan ƙasa da suka cancanta damar farawa da kammala rajistar masu zaɓe cike har da hoton yatsu ta hanyar amfani da na’urorinsu na kansu ba tare da zuwa ofishin INEC ba, kamar yadda gidan talabijin na Channels a Nijeriya ya ruwaito.

Ya ƙara da cewa tsarin ya ƙunshi ingantattun hanyoyin tabbatar da sahihancin bayanan mutum, tantance bayanan halittu da kuma matakan bincike na cikin gida domin kare aminci da kuma daidaiton Rijistar Masu Zaɓe ta Ƙasa.

“Domin ba wa ’yan ƙasa da suka cancanta amma har yanzu ba su yi rajista ba ƙarin dama, Hukumar ta tsawaita aikin zuwa ranar Jumma’a, 24 ga Yulin, 2026.

“Tsawaita wa’adin na nuna aniyar Hukumar na tabbatar da cewa kowane ɗan Nijeriya da ya cancanta ya samu dama mai kyau da adalci na shiga cikin Rijistar Masu Zaɓe gabanin zaɓuɓɓuka masu zuwa.