| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
An fitar da Amurka daga gasar Kofin Duniya bayan Belgium ta doke ta da ci 4-1
Belgium ta tsallaka zagayen kwatafainal inda za ta haɗu da Sifaniya, yayin da gasar Kofin Duniya ke ƙara ɗaukar zafi.
An fitar da Amurka daga gasar Kofin Duniya bayan Belgium ta doke ta da ci 4-1
Yan wasan Belgium na murna bayan sun zura kwallo a ragar Amurka a zagayen 'yan 16. / AP

A safiyar Talata, Belgium ta doke Amurka, ɗaya daga cikin masu masaukin baƙi na Gasar Kofin Duniya na FIFA 2026, a wani wasa na a zagayen ‘yan-16 da aka tashi 4-1.

Tawagar Belgium ta fara wasan da zafi-zafi, inda suka ci ƙwallon farko a minti na 9 ta hannun Charles De Ketelaere, kafin a minta na 31, ɗanwasan Amurka, Malik Tillman ya rama.

Sai dai mintu biyu bayan nan, De Ketelaere na Belgium ya ƙara ƙwallo guda ana minti na 31, inda aka tafi hutun rabin lokaci ana 2-1.

A zagayen farko, Belgium ce ta mamaye wasan, saboda Amurka ta kai hari sau biyu ne kacal, inda hari ɗaya ne kawai ya nufi raga.

A zagaye na biyu, Hans Vanaken ya ciyo wa Belgium ƙwallo ta uku a minti na 57, kafin gwarzon maci ƙwallo, Romelu Lukaku ya zura ta huɗu ana mintunan ƙarshen wasan.

Fuskantar Sifaniya

Ɗanwasan gaba na Amurka, Folarin Balogun, wanda aka jingine dakatarwar wasa guda da aka masa saboda jan kati, ya buga kusan duka mintinan wasan amma sau ɗaya kawai ya samu sa’ar kai bara a raga.

Tun da fari a ranar Litinin, shugabannin hukumar ƙwallo ta Belgium sun ƙalubalanci cancantar Balogun a wasan, amma FIFA ta yi watsi da ƙorafinsu gabaɗaya.

A yanzu dai fitar da Amurka daga gasar na nufin dukkan masu masaukin baƙi na gasar su uku sun yi waje, bayan da su ma Canada da Mexico suka yi rashin nasara a zagayen na ‘yan-16.

A zagayen gaba na kwatafainal, Belgium za ta fafata da Sifaniya ranar 10 ga Yuli, don neman gurbi a zagayen dab da wasan ƙarshe.