Amurka ta yi asarar kayayyakin sojin na kusan $2bn a kwanaki 4 na yaƙi da Iran
Abar da ta fi janyo asarar ita ce na’urar Amurka ta hango bayanai ta US AN/FPS-132 wadda ke sansanin sojin saman Amurka na Al Udeid da ke Qatar, wadda kimarta ta kai dala biliyan 1.1
Amurka ta yi asarar kayayyakin sojin da ƙimarsu ta kai kusan dala biliyan biyu a cikin kwana huɗu kacal na hare-haren da take kai wa Iran bisa ƙiyasi da kuma bayanan da kamfanin dillancin labaran Anadolu ya tattara.
Abar da ta fi janyo asarar ita ce na’urar Amurka ta hango bayanai ta US AN/FPS-132 wadda ke sansanin sojin saman Amurka na Al Udeid da ke Qatar, wadda kimarta ta kai dala biliyan 1.1, wadda wani makami mai linzami da Iran ta harba ya afka wa ranar Asabar.
Qatar ta tabbatar da cewa an taɓa na’urar kuma ta lalace.
Ranar Lahadi, Amurka ta yi asarar jiragen yaƙi uku samfurin F-15E Strike Eagle a wani yanayi na tsautsayi inda makaman tsaron sararin samaniyar Kuwait suka kakkaɓo su. Yayin da dukkan matuƙa jiragen shida suka tsira, jiragen ba su tsira ba; kuɗin maye gurbinsu zai kai dala miliyan 282, bisa ƙiyasi.
Lokacin da ta fara ramuwar gayya ranar Lahadi, Iran ta kai hari hedkwatar sojin ruwan Amurka ta biyar da ke Manama, a ƙasar Bahrain, inda ta lalata tashoshin sadarwa biyu da wasu manyan gine-gine.
Ta hanyar amfani da rahotannin sirri da mutane daban-daban suka tattara, an gano cewa tashoshin sadarwar da aka kai wa hari suna da na’urori AN/GSC-52B, waɗanda ƙimarsu ta kai dala miliyan 20, idan aka yi la’akari da kuɗaɗen ƙaddamarwa da haɗawa.
Iran ta kuma yi iƙirarin cewa ta lalata ɓangaren na’urar hango bayanai na tsarin kariya daga makamai masu linzami na THAAD wadda aka kafa a birnin masana’antu na Al-Ruwais a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Hotunan tauraron ɗan’adam da aka samo ta rahotannin bayanan sirrin da mutane daban-daban dama suka haɗa su nuna cewa an taɓa ta. An yi ƙiyashin cewa ɓangaren na’urar hango bayanan da aka lalata ya kai dala miliyan 500.
Idan aka haɗa waɗannan kuɗaɗen, a iya ganin cewa Iran ta lalata kayayyakin sojin Amurka da suka kai dala biliyan 1.902 a yankin Gabas ta Tsakiya.
Kawo yanzu Iran ta kai hari kan aƙalla wuraren sojin Amurka bakwai a faɗin Gabas ta Tsakiya tun da Amurka da Isra’ila suka fara kai hare-hare kan Iran ranar Asabar: Hedkwatar sojin ruwan Amurka ta biyar a Bahrain da sansanin sojin Arifjan da sansanin sojin saman Ali Al Salem da sansanin sojin Buehring a Kuwait, da sansanin sojin Erbil a Iraq da sansanin Jebel Ali Port na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, da kuma sansanin sojin ruwa mafi girma na Amurka a Gabas Ta Tsakiya da kuma sansanin sojin saman Al-Udeid a Qatar.
A Kuwait, hotunan da aka ɗauka sun nuna saman gine-ginen da suka rufta a wurare daban daban a cikin sansanin sojin sama na Ali Al Salem biyo bayan rahotannin wani harin Iran a ranar da ta wuce.
Sansanin sojin Arifjan shi ne wuri na farko inda aka kashe jami’an sojin Amurka shida . Wani bidiyo da aka yaɗa sosai wanda aka naɗa a cikin sansanin sojin Buehring a Kuwait ya nuna wani jirgi mara matuƙi da ke shawagi ta saman na’urar kafin ta fashe a cikin harabarta.
Bidiyo da hotunan da jaridar New York Times ta tabbatar sun nuna cewa Iran ta yi ta kai hari kan kayayyakin soji a filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa a Iraƙi, inda aka girke dakarun Amurka, daga ranar Asaar har ranar Lahadi. An ga hayaƙi da wuta daga wurin. Da safiyar Lahadi hotunan tauraron ɗan’adam sun nuna cewa an lalata gine-gine huɗu a wani ɓangaren sansanin, inda wuta ke ci gaba da ci zuwa safiyar Litinin.
Kazalika, hotunan tauraron ɗan’adam na ranar Lahadi a tashar jiragen ruwan Jebel Ali ta Dubai sun nuna hayaƙi na tashi daga wani babban gini a cikin harabar wurin shaƙatawa na sojin ruwan Amurka.
Duk da cewa ba sansanin sojin Amurka ba ne a hukumance, Jebel Ali daya ne daga cikin tashoshi jiragen ruwan da sojin ruwan Amurka ta fi amfani da su.
Baya ga sansaonin sojoji, ofisoshin jakadun Amurka a Saudi Arabia da Kuwait da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na cikin wuraren da aka kai wa hari.
Jirage mara matuƙi biyu sun afka wa ofishin jakadancin Amurka a Riyadh, da ke Saudiyya. Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta ba da rahoton "taƙaitacciyar gobara da lalacewar abubuwa kaɗan " ga harabar. Jaridar The Washington Post ta ce an afka wa ofishin hukumar leƙen asiri na CIA da ke cikin harabar.
An kuma kai hari kan ofishin jakadancin Amurka a birnin Kuwait na ƙasar Kuwait da jirgi mara matuƙi da kuma makamai masu linzami . An ba da rahoton ganin hayaƙi kusa da harabar , yayin da aka taƙaita bayanan abubuwan da suka lalace ga mutane.
An rufe ofishin jakadancin "har sai an sake ba da sanarwa" inda ake kuɓutar da ma’aikatan da ayyukansu ba su zaman dole ba tare da iyalansu.
Wani jirgi mara matuƙi da ake ganin na Iran ne ya afka wa babban ofishin jakadancin Amurka a Dubai, na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, inda ya afka wa wani wurin ajiye motoci da ke kusa da ofishin wani babban jami’i.
An fara gobara sai dai kuma hukumomin cikin ƙasar su kashe wutar cikin sauri. Ƙasan ofishin jakadancin ya taɓu, amma lamarin bai lalace gangar jikin ginin sosai ba.