Mun tuntuɓi Turkiyya domin neman agaji kan matsalar tsaro – Shugaban Nijeriya Tinubu

Tinubu ya kuma ce gwamnatinsa ba ta yin ƙasa a gwiwa a ƙoƙarinta ta dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar, “duk da dabarun yakin sunƙuru da ‘yanbindiga suke yi,” in ji shi.

By
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne yayin da shugabannin CAN suka kai masa ziyarar Kirsimeti a Legas ranar 25 ga Disamban 2025. / Reuters

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatin ƙasar ta nemi agajin Turkiyya a ƙoƙarin samar da tsaro a Nijeriya da ke fama da matsalolin tsaro da dama.

Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin da shugabannin Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) suka kai masa ziyarar Kirsimeti a gidansa da ke birnin Legas ranar Juma’a.

Wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Shawara kan Watsa Labarai Bayo Onanuga ya fitar ta ambato Tinubu yana cewa makaman soji suna da wahalar samu, ga tsada sannan ba a iya zuwa a sayo su nan take.

Ya kuma bayyana cewa jinkirin yana shafar yadda mutane suke kallon irin yadda gwamnatinsa take tunkarara matsalar tsaro a kasar.

“Jiragen helikwafta hudu da muka sayo daga Amurka za su ɗan ɗauki lokaci kafin su ƙaraso... Mun Tunkari Turkiyya domin neman taimako.”

Tinubu ya kuma ce gwamnatinsa ba ta yin ƙasa a gwiwa a ƙoƙarinta ta dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar, “duk da dabarun yakin sunƙuru da ‘yanbindiga suke amfani da su,” in ji shi.

Sanarwar ta kuma ambato shugaban yana bayyana kudirinsa na tabbatar da samar da rundunar ‘yansandan jihohi, don sauya tsarin tsaron kasar.

“Da zarar Majalisun Dokoki sun kammala ɗaukan matakan da ake buƙata, za a samar da ‘yansandan jihohi da na al’umma,” a cewar Shugaba Tinubu.