Ga mutane da yawa, tsufa wani abu ne da kan iya zuwa ga wasu daban, har sai mutum ya fara ganin furfurar farko ta fito masa idan ya kalli madubi, ko kuma ya fara jin sabon ciwo a gaɓɓansa.
A wannan lokacin ne, tsufa zai daina zama abin hasashe kawai; sai ya zama wani mataki na rayuwa da ya kamata a fara shiryawa. A yau, Afirka na kallon wannan madubi.
Nahiyar da aka taɓa kiran ta da "nahiyar matasa ta duniya", tana dab da samu wani gagarumin juyi a ɓoye. Afirka na tsufa, amma tana yin hakan ba tare da hanyoyin kariya na dukiya ba, da ginannen tsarin zamantakewa, ko tsarin fansho da na kula da lafiya.
Duk da cewa adadin haihuwa yana da yawa a wasu yankuna, a yanzu Afirka kudu da Sahara ba ta da kariya daga sauyin tsarin al’umma na duniya. Nan da 2030, mutum guda cikin mutane shida a duniya zai kasance mai shekaru fiye da 60 ko sama da haka. Afirka na daga cikin yankunan da suka fi ƙarancin shirya wa wannan gaskiyar.
Babbar matsalar ba tsufa ba ce, amma tsufa yayin da ma’aunin GDP na ɗaiɗaiku sau da yawa ba ya wuce ma'aunin dala $2,000. A mafi yawan sassan nahiyar, tsarin fansho ko dai babu shi ko kuma yana taƙaita. Tsofaffi kusan gabaɗaya suna dogara ne ga tallafin iyali, domin kulawa daga gwamnati kusan tatsuniya ce.
Har ila yau, tsarin kiwon lafiya ya fi mai da hankali kan matsalolin gaggawa fiye da rikirkitacce yanayin lafiyar tsaffi.
Afirka da batun tsufa
Ga miliyoyin mutane a karkara, tsufa ba alamar lokacin ritaya ba ne; alamar ƙarshen samun kuɗi a-kai-a-kai ne. Yayin da ƙarfin jiki ke raguwa, daina aiki yawanci ba zaɓi ba ne. Tsira, ba hutu ba, shi ne babban buri.
Rashin tabbas na wannan hali ya ƙaru saboda rashin kulawar cibiyoyin gwamnati. Gidajen jinyar tsofaffi ba wai kawai kaɗan ne a zahiri ba, a al'ada sau da yawa ana ɗaukar su a matsayin alamar watsi da mutum.
Yayin da ake muhawara game da irin waɗannan cibiyoyi a Yammacin duniya, a Afirka sau da yawa ba ma a kallon su a matsayin zaɓi ne. Idan tsarin iyali ya rushe, babu hanyar tsaro da ke riƙe wanda ya gajiya.
Ƙona ɗakunan karatu
"A Afirka, duk lokacin da wani dattijo ya mutu, to tamkar an ƙone wani ɗakin karatu ne." in ji Amadou Hampâté Bâ, shahararren marubucin nan ɗan ƙasar Mali.
A al'ummomin Afirka, tsofaffi ba kawai mutane ne da ke buƙatar kulawa ba; su ne masu riƙe hikimar noma, tarihin baka, da hanyoyin sasanta rikice-rikice na gida. Suna taka rawa a matsayin masu sasantawa kuma suna bayar da wani nau'i na tsaron zamantakewa ta hanyar kula da jikoki, wanda ke bai wa iyaye matasa damar fita aiki.
Sai dai wannan “tsarin na tsawon zamuna” yana zagwanyewa. Saurin faɗaɗar birni da yin ƙaura duk da yana iya kawo cigaban tattalin arziƙi, amma yana rusa tubalin zumuncin gargajiya da aka gina tsawon ƙarni. Yayin da matasa ke ƙaura zuwa manyan birane ko ƙasashen waje don neman ilimi da aiki, tsofaffi kan zauna a ƙauyuka a kaɗaice kuma cike da nauyin rashin tallafin zamantakewa.
Bashin kulawa
A wani nazarinta mai muhimmanci, mai taken “Intergenerational Support and Old Age in Africa”, Isabella Aboderin ta kafa hujjar cewa kulawa da tsofaffi yana canjawa daga na zallar wajibin ɗabi'a zuwa tsarin "musayar kadara ta zahiri".
Ta nuna cewa ƙaura ko ilimin mutum yana yawan zama wani zuba jari daga asusun ajiyar tsofaffi. A irin wannan yanayi, tallafi ga tsaffi ana kallon sa ƙasa da ma’aunin danƙon soyayya, zuwa matsayin biyan bashi na zamantakewa da ba a faɗa a fili ba.
Idan iyali ba su iya yin wannan saka hannun jari na farko ba, haɗarin watsar da tsofaffi a lokacin tsufa na ƙaruwa sosai.
Taɓarɓarewar waɗannan tsarin tallafi na gargajiya ba wai kawai tana barin tsofaffi cikin kaɗaici ba; sau da yawa tana tilasta musu yin ayyukan da ba su dace da ƙarfinsu ba.
Wannan canjin tsarin ya haifar da yawaitar "gidajen da aka tsallake ƙarni", inda tsofaffi ba su tsaya ƙwarai a matsayin masu hikima kawai ba, amma suna zama masu kulawa ga jikoki saboda rashin ‘yan tsakiyar ƙarni, wato ‘ya’yansu a kusa.
Suna gamuwa da raunin jiki na kansu yayin da suke zama ginshiƙi na ƙarshe a cikin tsarin zamantakewa da ke rushewa.
Hanyar Afirka ta cigaba
Babu wata hanyar ɗaya da ta yi daidai ga kowa don magance matsalar tsufa a Afirka. Wataƙila wannan shi ne muhimmin batu. Ba lallai ba ne Afirka ta kwafi tsarin Yamma da aka gina a hankali kuma wand ke da matsalolinsa.
Tarihin Afirka na yawan "tsallaka matakai", misali tsalle kai-tsaye zuwa tsarin bankin tafi-da-gidanka ba tare da rassan banki na gargajiya ba, ko sadarwa ta dijital ba tare da ta tarho ba, yana nuna cewa akwai damar ƙirƙirar mafita ta musamman.
Don fuskantar ƙalubalen kula da tsofaffi, nahiyar ya kamata ta wuce kallon wannan al'amari a matsayin nauyin ɗabi'a na iyali kawai, ko nauyin gwamnati. Karɓar falsafar "Ubuntu", wadda ke jaddada haɗin-kain al'umma, na iya zama tushe wajen sake tunani kan batun tsufa.
Ta hanyar amfani da hanyoyin mu’amala na al'umma da ake da su da tsarin unguwanni da ke akwai, zai yiwu a gina wani samfurin Afirka na ba da kulawa mai cike da haɗin-gwiwa. Nahiyar na cikin wani gagarumin sauyi cikin sauri, a cakuɗe, amma mai cike da fkira.
Tambayar ba wai kawai ita ce: "Me Afirka za ta yi?" ba; tambayar ita ce: Ta yaya Afirka za ta magance batun tsufa bisa sharuɗɗanta ta hanyar ƙirƙirar mafitar da ta dace da zahirin lamarinta da burinta?















